Zanga zanga: Iyalan Matashin da aka Kashe a Kano Sun Mika Bukata 1 ga Gwamnati

Zanga zanga: Iyalan Matashin da aka Kashe a Kano Sun Mika Bukata 1 ga Gwamnati

  • Iyalan wani matashi Bashir Muhammad Lawan da jami'an tsaro suka kashe a Kano sun roki gwamnati ta bi kadin jinin dan uwansu
  • An ce jami'an tsaro sun kashe akalla masu zanga zanga takwas a Rijiyar Lemo da Kurnar Asabe da ke Kano a arangamarsu ranar Asabar
  • Muhammad Lawan, mahaifin matashin ya ba da labarin yadda aka kashe dansa yayin da kanwar Bashir, Khadija ta nemi ayi musu adalci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Daya daga cikin iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a zanga-zangar yunwa da aka yi a Kano a makon jiya ta bukaci a yi musu adalci.

Rahoto ya nuna cewa an kashe akalla mutane takwas a arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a Rijiyar Lemo da Kurnar Asabe da ke Fagge a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Bayan rasa rayuka, masu zanga zanga sun fara alkunutu a Kano

Iyalan matashin da jami'an tsaro suka kashe a Kano lokacin zanga-zanga sun yi magana
Iyalan matashin da aka kashe wajen zanga-zanga a Kano sun nemi ayi musu adalci. Hoto: @Miniko_jnr
Asali: Twitter

Iyalan wani matashi Bashir Muhammad Lawan, mai shekaru 25 da aka kashe a Rijiyar Lemo, kan titin Katsina sun yi magana da jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyalan sun bayyana cewa an kashe dansu Bashir ne a lokacin da yake gudanar da zanga-zanga bisa ga 'yanci da dokar kasa ta bashi a matsayinsa na dan Najeriya.

"Yadda aka kashe 'dana Bashir" - Mahaifi

Malam Muhammad Lawal, mahaifin Bashir, ya ba da labarin cewa an kashe dansa mintuna sha biyar kacal da barin gida domin shiga zanga-zangar.

Ya kara da cewa wasu matasa da dama da suka hada da mata da kananan yara ne ake zargin ‘yan sanda sun harbe su a ranar.

“Yana daga cikin masu daga kwalaye a lokacin zanga-zangar wadda aka yi cikin lalama har zuwa lokacin sallar Azahar inda jami’an tsaro suka zo domin tarwatsa su.

Kara karanta wannan

Zargin kashe masu zanga zanga: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamitin bincikar jami'an tsaro

"Suna ta ihun ‘bama yi, bama yi’ daga nan sai jami’an tsaro suka fara harbi, a sakamakon haka, harsashi ya sami Bashi dana".

- A cewar mahaifin matashin.

"Muna rokon abi kadin jininsa" - Khadija

Khadija Bala, kanwar Bashir, ta ce yana gudu ne domin ya fake da lokacin da harbin bindigar ya same shi.

"Sun fita yin zanga-zangar lumana ne kawai amma aka yi musu lakabi da 'yan daba'. Shikenan talaka ba shi da 'yancin yin zanga-zanga?
"Mu kawai rokonmu shi ne a yiwa dan uwanmu da aka kashe adalci, lallai abi kadin jinisa da aka zubar ba bisa ka'ida ba."

- A cewar Khadija yayin da take sharbar hawaye.

Gwamnatin Kano za ta kafa kwamitin bincike

Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ta ce za ta kafa wani kwamitin shari'a da zai binciki yadda jami'an tsaro suka gudanar da ayyukansu a jihar a lokacin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Yadda yan sanda suka hallaka Bayin Allah lokacin zanga zanga a jihar Kano

Gwamnatin ta dauki wannna matakin ne bayan rahoton da aka samu na cewa jami'an tsaro sun budewa masu zanga-zanga wuta a Rijiyar Lemo da Kurnar Asabe da ke karamar hukumar Fagge.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.