Farfesa Ya Tona Ainihin Masu Ɗaga Tutocin Ƙasar Rasha Wajen Zanga Zanga

Farfesa Ya Tona Ainihin Masu Ɗaga Tutocin Ƙasar Rasha Wajen Zanga Zanga

  • Matasan Arewacin Najeriya sun ɓullo da al'amari na daban yayin gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Tinubu
  • An hango dandazon matasa a Kano da Kaduna da wasu sassan Arewacin kasar dauke da tutar kasar Rasha, su na neman daukin Vladimir Putin
  • Amma tsohon shugaban cibiyar harkokin ƙasashen waje (NIIA), Farfesa Bola Akinterinwa ya bayyana cewa ba 'yan Najeriya ne ke ɗaga tutar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban cibiyar harkokin ƙasashen waje (NIIA), Farfesa Bola Akinterinwa ya bayyana cewa matasan da ke daga tutar Rasha ba 'yan Najeriya ba ne, daga ketare su ke.

Kara karanta wannan

Kasar Rasha ta yi magana kan masu zanga zangar da ke ɗaga tutocinta a Najeriya

Tsohon shugaban ya fadi haka biyo bayan yadda aka gano matasa masu zanga-zanga a Arewacin kasar dauke da tutar ƙasar Rasha, su na neman daukinta yayin adawa da manufofin Tinubu.

Rasha
An gargadi Tinubu a kan daga tutar Rasha a Najeriya Hoto: Mustapha Muhammad Kankarofi
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Farfesa Akinterinwa ya kara da cewa 'yan Nijar ne ke rike da tutar saboda nuna rashin jin dadin yadda ECOWAS ke takurawa juyin mulkin soja a kasarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daga tutar Rasha izina ce," Farfesa Akinterinwa

Farfesa Farfesa Bola Akinterinwa ya gargadi gwamnatin Najeriya da cewa babbar izina ce lamarin da ke faruwa a lokacin zanga-zanga, Sahara Reporters ta wallafa.

Matasa a jihar Kano da wasu sassan kasar nan sun fara daga tutar kasar Rasha wanda ya dauki hankalin hukumomin tsaro da kusoshin gwamnatin tarayya.

Ya ce daga tutar Rasha zai iya jawo takun saka tsakanin Najeriya da Ukraine, wanda hakan babbar barazana ce ga diflomasiyyar kasashen biyu. da a yanzu su ke cikin zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An kama mutumin da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano

Rasha ta magantu kan daga tutarta a Najeriya

A wani labarin kun ji cewa ofishin jakadancin kasar Rasha da ke Najeriya ya musanta masaniya a cikin bukatar 'yan Najeriya na kasar ta kawo masu dauki a lokacin da su ke gudanar da zanga zanga.

Ofishin jakadancin ya bayyana cewa ya samu rahotannin yadda matasan Najeriya ke rera taken kasar da neman tallafin shugabanta, Vladimir Putin, amma sun barranta kansu daga bukatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.