Dokar Takaita Fita: Jami'ar BUK Ta Dauki Matakin Kare Dalibai a Kano

Dokar Takaita Fita: Jami'ar BUK Ta Dauki Matakin Kare Dalibai a Kano

  • Mahukuntan jami'ar Bayero da ke jihar Kano sun dauki matakin saukakawa dalibai yayin da zanga-zanga ya jawo dokar hana fita a jihar
  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ce ta fara ayyana dokar hana fita ta awanni 24 a yammacin Alhamis, amma daga bisani aka sassauta
  • A yanzu haka rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana sassauta dokar zuwa ta takaita zirga-zirga daga 8.00a.m zuwa 2.00pm

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Mahukunta a jami'ar Bayero ta Kano sun bayyana sassautawa daliban jami'ar saboda dokar takaita zirga-zirga.

Rundunar 'yan sandan Kano ce ta bayyana cewa mutanen jihar za su iya fita daga 8.00a.m- 2.00pm biyo bayan tashe-tashen hankula saboda zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan sanda sun jaddada dokar hana fita a Katsina

Jami'a
Jami'ar Bayero ta dakatar da daukan darussa Hoto: Bayero University Kano
Asali: UGC

Ta cikin sanarwar da jami'ar ta wallafa a shafinta na Facebook, dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'arta Lamara Garba, za a dakatar da ɗaukan darussa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe daliban BUK za su koma karatu?

Lamara Garba ya bayyana cewa su na sane da dokar takaita zirga-zirga ba ta awanni 24 ba ce.

Ya shaidawa Legit cewa amma ba dukkanin dalibansu ne za su samu abin hawa har su samu damar daukar darussa ba.

Jami'in BUK ya ce za su ci gaba da zama a gida har sai gwamnati ta dage dokar takaita zirga-zirga a fadin jihar.

Wane tanadi aka yi wa daliban BUK?

Jami'in hulda da jama'a na jami'ar Bayero ya ce an sanya matakan tsaron lafiyar daliban da ke zaune a cikin makaranta.

Lamara Garba ya bayyana damuwarsu a kan lafiya da kare rayukan daliban BUK, saboda haka ya hore su da su yi taka tsan-tsan musamman a wajen jami'ar.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Bayan rasa rayuka, masu zanga zanga sun fara alkunutu a Kano

Dalibai sun yi zanga-zanga a Bangladesh

A baya mun kun ji cewa dalibai a Bangladesh sun yi akalla wata daya su na zanga-zanga saboda kin amincewa da yadda gwamnati ta raba guraben aiki.

Zanga-zangar ta yi ƙamari, har an kashe mutane 300, amma daga bisani matasan su ka yi fatali da dokar hana fita har firayim ministar kasar ta yi murabus.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.