Kwankwaso: Alhassan Doguwa Ya Yi Wa Dan Majalisar NNPP Wankin Babban Bargo

Kwankwaso: Alhassan Doguwa Ya Yi Wa Dan Majalisar NNPP Wankin Babban Bargo

  • Alhassan Ado Doguwa ya fito ya yi martani ga ɗan majalisar jam'iyyar NNPP, Honarabul Abdulmumin Jibrin Kofa
  • Ɗan majalisar mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada a majalisar wakilai ya bayyana cewa Jibrin ba sa'arsa ba ne domin ya yi masa fintinkau
  • Doguwa ya buƙaci ɗan majalisar da ya mutunta shi kamar yadda yake son ya mutunta ubangidansa, Rabiu Musa Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da albarkatun man fetur, Alhassan Ado Doguwa, ya mayar da martani ga Abdulmumin Jibrin Kofa.

Alhassan Ado Doguwa ya mayar da martanin ne bisa zargin cewa ya ci mutuncin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Doguwa ya caccaki Abdulmumin Jibrin Kofa
Alhassan Ado Doguwa ya yiwa Abdulmumin Jibrin martani Hoto: Alhassan Ado Doguwa
Asali: Twitter

A wata sanarwa da ya fitar, Ado Doguwa ya bayyana cewa yana mutunta Kwankwaso duk da saɓanin da ke tsakaninsu a siyasance, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kwankwaso ya bayyana wanda zai dauki alhakin barnar da aka yi a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa kalaman cin mutunci da Kwankwaso ya yi game da shugabannnin jam'iyyar APC ya sanya ya gargaɗi madugun na Kwankwasiyya.

Alhassan Doguwa ya caccaki Jibrin Kofa

"Na kasance a majalisar wakilai tun lokacin da Jibrin yake makaranta. Domin haka ina fatan ya girmama ni kamar yadda yake so na girmama uban gidansa Kwankwaso."
"Honarabul Jibrin ba sa'a ta ba ne kuma ba zai iya kamo ƙwarewar da na ke da ita a majalisa ba, wacce ta fi ta shi a kowane fanni."

- Alhassan Ado Doguwa

Alhassan Doguwa ya kuma buƙaci Kwankwaso da ya riƙa mutunta sauran shugabanni sannan ya daina tunzura matasa suna ɗaukar doka a hannunsu.

Meyasa Doguwa ya yiwa Kwankwaso martani?

Ya nuna cewa akwai wani bidiyo da ya yaɗu wanda Kwankwaso ya zagi shugabannin APC a jihar Kano, inda ya kira su da "banzaye", rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Wani malamin addini ya gayawa Tinubu gaskiya, ya fadi babbar matsalar gwamnatinsa

"A bisa hakan na yi martani ta hanyar nuna masa kuskurensa. Na lashe zaɓen kujerar ɗan majalisa sau bakwai tun daga shekarar 1992 lokacin da Farfesa Humphrey Nwosu yake shugaban hukumar zaɓe."
"Mutanen mazaɓata suna ci gaba da bani ƙuri'unsu kuma ban ba su kunya ba, sannan Insha Allah ba zan ba su kunya ba."

- Alhassan Ado Doguwa

Kotu ta buƙaci a biya Doguwa diyya

A wani labarin kuma, kun ji babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan korafin Gwamna Abba Kabir a Kano kan zargin Alhassan Doguwa da ta'addanci.

Mai Shari'a, Donatus Okorowo yayin hukuncin ya umarci Abba Kabir ya biya diyyar miliyan 25 saboda ba ta suna da kuma jefa Doguwa cikin ƙunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng