Matsin Rayuwa: Bayan Rasa Rayuka, Masu Zanga Zanga Sun Fara Alkunutu a Kano

Matsin Rayuwa: Bayan Rasa Rayuka, Masu Zanga Zanga Sun Fara Alkunutu a Kano

  • Bayan an samu barkewar rikici yayin zanga-zanga a Kano wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama, jama'a sun koma ga Allah
  • A yau Litinin ne jama'a su ka fara taruwa domin neman dauki Ubangiji SWT cikin lamarin da ke daukar sabon salo a yanzu
  • Wannan na zuwa ne bayan an samu rahoton asarar rayuka a unguwanni da dama ciki har da Kurna da Rijiyar Lemo

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jama'ar Kano sun fara hallara domin gudanar da sallah ganin yadda zanga-zangar lumana ta rikide zuwa tashe-tashen hankula da kashe-kashe.

Wata kungiyar matasa a Kano da ta nemi gangamin addu'ar ta bayyana cewa mutane sun fara taruwa a unguwanni daban-daban domin neman dauki Allah SWT.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga na daga tutar Rasha a Kaduna, an fara awon gaba da kayan jama'a

Sallah
Masu zanga zanga za su yi azumi, sallah a Kano Hoto; Abubakar Dabo Umar
Asali: Facebook

Mubarak Ibrahim, jagoran taron addu'ar ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa za su gudanar da sallah da addu'o'i domin neman gafarar Ubangiji da neman dauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: Za a yi azumi a Kano

Jagoran taron addu'o'in, Mubarak Ibrahim ya bayyana cewa sun ware ranar 12 Agusta, 2024 domin gudanar da addu'o'in neman dauki, Daily Trust ta wallafa.

Ya ce kalaman shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba su nuna akwai alamun za a sassautawa talakawan kasa ba.

" Za mu fara ranar Juma'a a dukkanin kasar nan, za mu karanta Al'kurni har zuwa ranar Asabar, ranar Litinin mu tashi da Azumi."
"Yanzu haka mu na tattaunawa da malaman addinin musulunci domin samun wuraren da za a yi taron addu'o'in."

- Mubarak Ibrahim

An kashe masu zanga-zanga

A baya mun ruwaito yadda aka shiga fargaba bayan jami'an tsaro sun harbi mutane da dama a unguwannin Kurna da Rijiyar Lemo yayin kora masu zanga-zanga a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Bayan Legas: Matasan wata jihar Kudu sun ji kiran Tinubu, sun dakatar da zanga zanga

An gano mutanen da aka kashe bayan shahararren dan jarida, Jafar Jafar ya nemi karin bayani a kan wadanda aka kashe a unguwannin, daga cikin wadanda su ka rasu har da yara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.