Shugaban HEDA ya Lissafa Ma’aikatu 3 mafi Shahara a Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Shugaban HEDA ya Lissafa Ma’aikatu 3 mafi Shahara a Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

  • Shugaban kungiyar HEDA, Olarenwaju Suraju, ya bayyana bangaren shari’a a matsayin daya daga cikin mafi karbar cin hanci da rashawa a Najeriya
  • Suraju ya caccaki ‘yan majalisa da masu rike da mukaman gwamnati da cin hanci da rashawa, inda ya bada misali da sayar da shinkafar tallafi
  • Ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya dauki mataki na yaki da cin hanci da rashawa da kuma dawo da amanar jama’a a wadannan ma'aikatu da ake zargi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kungiyar bunkasar dan Adam da muhalli (HEDA), Olanrewaju Suraju, ya bayyana bangaren shari’a a matsayin daya daga cikin ma'aikatun da suka fi cin hanci da rashawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Kwararren mai yaki da cin hanci da rashawan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa ta musamman da jaridar Legit.ng a ranar Asabar, 3 ga watan Agusta.

Shugaban HEDA, Suraju ya fadi ma'aikatun da aka fi cin hanci da rashawa a Najeriya
Shugaban kungiyar HEDA, Suraju ya yi magana kan cin hanci da rashawa a Najeriya. Hoto: @HEDAgenda
Asali: Twitter

Suraju ya jaddada cewa bangaren shari’a, wanda ya kamata ya zama mai bin diddigin sauran rassan gwamnati da kuma bin diddigin al’amuran gwamnati, shi ne ya ke fama da matsalar cin hanci da rashawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cin hanci da rashawa a ma'aikatun Najeriya

Suraju ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar da yin garambawul a bangaren shari'a.

Ya kuma bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su mayar da hankali kan ayyukan alkalai da magatakarda da sauran masu ruwa da tsaki a harkar shari’a.

Suraju ya soki bangaren majalisar dokoki da wadanda gwamnati ta nada (Ministoci) kan ayyukansu na cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da 'mummunan mulki': 'Yan Najeriya sun yi martani ga jawabin Tinubu

Ya ba da labarin wani lamari mai tayar da hankali inda wani minista ya sayar da shinkafar da aka yi niyyar rabawa jama’a a matsayin tallafi.

An bukaci Tinubu ya yaki cin hanci

Suraju ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya dauki kwakkwaran mataki kan cin hanci da rashawa a wadannan ma'aikatu.

Ya kuma jaddada cewa, sauyi mai inganci yana bukatar magance wadannan batutuwan gaba daya domin hana ci gaba da tabarbarewar amanar jama'a da inganta harkokin mulki.

"Dole ne shugaban kasa ya yi taka-tsan-tsan domin magance cin hanci da rashawa da kuma maido da amanar jama'a a cikin wadannan manyan ma'aikatu."

- Olanrewaju Suraju

Edo: An tsige ciyaman kan rashawa

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa, majalisar karamar hukumar Egor a jihar Edo ta tsige shugaban karamar hukumar, Hon. Eghe Ogbemudia.

Wannan hukuncin ya biyo bayan kuri'ar rashin cancantar ciyaman din da kansilolin suka kada a ranar Talata, 16 ga watan Yuli sakamakon kama shi da laifin tafka rashawa a kasafin karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan yiwuwar dawo da tallafin mai a jawabinsa, bayanai sun fito

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.