Zanga Zanga: Abubuwa 9 Masu Muhimmanci daga Jawabin Shugaba Tinubu ga 'Yan Najeriya

Zanga Zanga: Abubuwa 9 Masu Muhimmanci daga Jawabin Shugaba Tinubu ga 'Yan Najeriya

Abuja - A jawabin kai tsaye da ya yi a ranar Lahadi, 4 ga Agusta, Shugaba Bola Tinubu ya yi tsokaci kan zanga-zangar yunwa da ake yi, inda ya fadi matakan da gwamnatinsa ta dauka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wannan jawabin na kai tsaye na zuwa ne a lokacin da 'yan kasar suka shiga rana ta hudu a zanga-zangar adawa da 'gurbatacciyar gwamnati' da suke yi saboda tsadar rayuwa da yunwa.

Daga cikin jawabin da Shugaba Tinubu ya yi, Legit Hausa ta tattaro wasu muhimman abubuwa tara da ya kamata 'yan Najeriya su lura da su.

Abubuwa 9 daga jawabin Tinubu kan zanga-zangar da ake yi a kasar
Shugaba Tinubu ya yi jawabi ga yan Najeriya a ranar Lahadi 4 ga watan Agusta. Hoto: KOLA SULAIMON/AFP
Asali: Getty Images

Muhimman abubuwa tara daga jawabin Shugaba Bola Tinubu:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

1. Tinubu ya nemi a dakatar da zanga-zanga

Shugaba Tinubu ya yi kira da a dakatar da zanga-zangar da ake yi cikin gaggawa, inda ya bukaci masu zanga-zangar da su zauna teburin tattaunawa da gwamnati.

Ya bayyana bakin cikinsa kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi a yayin zanga-zangar tare da jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.

2. Tinubu ya yi gargadi game kabilanci

A jawabinsa na kai tsaye, Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da nuna kyamar kabilanci tare da gargadar mutanen da ke yiwa wasu kabilu barazana da su daina, inda ya ce doka za ta yi musu hukunci.

Kalaman na Tinubu ya biyo bayan wasu rubuce-rubuce da aka wallafa a shafukan sada zumunta na neman ‘yan kabilar Ibo su fice daga jihar Legas da kuma ‘yan asalin yankin Kudu maso Yamma da su bar yankin Kudu maso Gabas.

Shugaban ya jaddada cewa irin wannan barazanar ba ta da gurbi a Najeriya, kuma ya zama wajibi kowanne dan kasa ya kiyaye dokokin kundin tsarin mulkin kasar.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya gama jawabi": Miyagu sun watsa masu zanga zanga, sun fadi dalili

3. Tinubu ya ji koken 'yan Najeriya

Shugaban ya fahimci takaici da wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta, inda ya alakanta hakan da kalubalen tattalin arziki da rashin shugabanci na gari.

Tinubu ya nuna tausayawa ga halin da ‘yan kasa ke ciki, inda ya yi alkawarin magance matsalolinsu ta hanyar yin garambawul ga manufofinsu.

4. Tinubu na zargin wasu 'yan siyasa

Shugaba Tinubu ya kuma yi nuni da cewa akwai makirce-makircen wasu tsirarun mutane domin samun riba a siyasance daga zanga-zangar yunwa da ake yi.

"A bisa rantsuwar kama aiki da na yi na kare rayuka da dukiyoyin kowanne dan kasa, gwamnatinmu ba za ta kyale wasu tsiraru masu mummunar manufa ta siyasa su wargaza wannan al’umma ba.”

- A cewar Tinubu.

5. Tinubu ya kore dawo da tallafin fetur

Shugaba Tinubu ya kuma kore batun maido da tallafin fetur, wanda hakan na daya daga cikin manufofin zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tinubu ya dauki alkawari 1 yayin da ya fallasa shirin wasu 'yan siyasa

Ya bayyana cewa cire tallafin abu ne mai raɗaɗi amma matakin ya zama wajibi domin magance matsalar tattalin arziki da kuma ci gaban kasar.

6. Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda aka kashe

Shugaba Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwan ​​wadanda suka rasa rayukansu a yayin zanga-zangar, ya kuma bukaci a gaggauta kawo karshen tashin hankalin.

Tinubu ya ce:

"Ina mika ta'aziyya ga iyalai da 'yan uwan ​​wadanda suka mutu a zanga-zangar nan, dole ne mu kawo karshen zubar da jini, tashin hankali da barna."

7. Tinubu ya yi magana manufofin tattalin arziki

Shugaba Tinubu ya bayyana ci gaban tattalin arzikin da gwamnatinsa ta samu, inda ya ce:

“Jimillar kudaden shiga na gwamnati sun ninka fiye da ninki biyu, wanda ya kai sama da Naira tiriliyan 9.1 a rabin farkon shekarar 2024 idan aka kwatanta da rabin farkon shekarar 2023.”

Ya ambaci manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa da ake yi, wadanda suka hada da babbar hanyar Legas zuwa Calabar da ke gabar teku da babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.

Kara karanta wannan

Tinubu ya manta da musabbabin zanga-zanga, ya tura sako ga iyalai a Najeriya

Tinubu ya kuma bayar da rahoton karuwar hako mai zuwa ganga miliyan 1.61 a kowace rana tare da sabunta sha’awar masu zuba jari a fannin.

8. Tinubu ya yi magana kan bunkasa matasa

Shugaba Tinubu ya bayyana wasu shirye-shirye da ya kaddamar domin bunkasa matasa, ciki har da shirin bayar da lamuni ga dalibai, shirin Digital & Creative Enterprises da sauran su.

Bugu da kari, shugaban ya bayyana shirin samar da gidaje 100,000 a cikin shekaru uku masu zuwa a karkashin shirin Renewed Hope City and Estate, wanda ke da nufin magance bukatun gidaje.

9. Tinubu ya magantu kan samar da abinci

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana wani gagarumin shiri na inganta samar da abinci a Najeriya.

Shirin ya hada da cire haraji kan wasu nau'ikan kayan abinci domin karfafa samarwa da wadatarsu da kuma rarraba kayan aikin noma domin tallafawa manoma.

Duba jawabin a nan kasa:

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi ya bayyana mummunar illar da zanga zanga ta jawo a Kano da Arewa

An ba Tinubu lakanin hana zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa lauyan kare haƙƙiin ɗan Adam, Inibehe Effiong, ya bayyana abin da ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya yi domin shawo kan matasa masu zanga-zanga.

Inibehe Effiong ya yi nuni da cewa daga cikin abin da ya kamata Tinubu ya yi ciki har da rage yawan ministocin da ke cikin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.