Kungiya ta Fallasa Shirin APC na Kwace Zanga Zangar Adawa da Tinubu, an Gargadi Matasa

Kungiya ta Fallasa Shirin APC na Kwace Zanga Zangar Adawa da Tinubu, an Gargadi Matasa

  • Kungiyar Edolites for Peace and Progress (EPP) karkashin Adesua Odigie ta zargi APC da yunkurin kwace zanga-zangar da ake yi a Edo
  • Kungiyar ta yi zargin cewa APC na shirin hurowa gwamnatin PDP a jihar wuta ta hanyar kwace zanga-zangar domin wata manufar siyasa
  • Kungiyar EPP ta yi kira ga mazauna Edo da su rungumi zaman lafiya da hadin kai yayin da take nuna goyon baya ga gwamnatin PDP a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo, Benin City - Kungiyar Edolites for Peace and Progress (EPP) karkashin Adesua Odigie ta zargi APC da yunkurin kwace zanga-zangar yunwa da ake yi a jihar Edo domin cimma manufar siyasa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: CUPP ta bayyana babban kuskuren da zai iya jefa Tinubu a matsala

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, EPP ta yi ikirarin cewa APC na yunkurin bata sunan gwamnatin PDP mai mulki a jihar ta hanyar kwace zanga-zangar lumanar tare da rikidar da ita zuwa wani abun daban.

Kungiyar EPP ta yi magana kan shirin APC a Edo yayin zanga-zanga
Kungiyar EPP ta yi ikirarin cewa APC na shirin kwace zanga-zangar yunwa a Edo. Hoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto
Asali: Getty Images

EPP ta zargi APC da kwace zanga-zanga

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa shugabar kungiyar EPP, Ms Odigie ta yi ikirarin cewa yunkurin APC na kwace zanga-zangar na da nasaba da son bata sunan gwamnatin PDP a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta kuma zargi APC da kokarin sauya manufar zanga-zangar lumanar da ake yi kan yunwa zuwa wani abu na daban da zai kai ga tashin hankula.

Ta yi kira ga APC da ta gaggauta dakatar da duk wani shirin siyasa da take yi kan masu zanga-zangar tare da nemo hanyoyin magance matsalolin tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Kiristoci sun ba Musulmai masu sallar Juma'a kariya ana tsaka da zanga zanga

Ms Odigie ta bayyana cewa:

"Mun samu rahoton cewa jam'iyyar APC na kokarin sauya manufar zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ake yi domin cimma wata manufarta ta siyasa."

Edo: EPP ta nemawa PDP alfarma

Kungiyar EPP ta roki matasan da ke zanga-zangar yunwa a Edo da su ci gaba da goyawa gwamnatin PDP mai ci a jihar.

Ta kuma yi kira ga daukacin al'ummar Edo da su kasance masu zaman lafiya da hadin kai domin gina rayuwa mai inganci da makomai mai kyau, inji rahoton News Direct.

"A irin wannan mawuyacin lokaci, yana da kyau dukkanin masu ruwa da tsaki su hadu waje daya su yi aiki tare domin samun kyakkyawar makoma a jihar Edo," a cewar sanarwar.

Zanga-zanga: Kiristoci sun ba Musulmai kariya

A wani labarin, mun ruwaito cewa an ga Kiristoci su na ba Musulmai kariya a lokacin da suka gabatar da Sallar Juma'a ana tsada da zanga-zanar yunwa a garin Osogbo.

A cikin bidiyon wanda aka nade shi a rana ta biyu ta zanga-zangar, an ga hadin kai da kuma kaunar juna tsakanin mabiya addinan a jihar Osun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.