Limami Ya Fusata a Mimbari, Ya Ragargaji Malaman da Suka Tallata Tikitin Muslim Muslim

Limami Ya Fusata a Mimbari, Ya Ragargaji Malaman da Suka Tallata Tikitin Muslim Muslim

  • Sheikh Abubakar Umar Musa Rijiyar Lemu ya yi kaca-kaca da takwarorinsa da suka tallata tikitin APC a zaben bara
  • Malam Abubakar Kandahar ya ce babu komai a tikitin Muslim-Muslim illa yaudara, a yau kuma ana cikin kunci a Najeriya
  • Malamin addinin ya soki mutanen da aka ba su kuɗi, taliya da atamfa suka zabi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Sheikh Abubakar Umar Musa Rijiyar Lemu wanda aka fi sani da Iman Kandahar ya yi huduba da ta zagaye kusan ko ina.

Yanzu haka ana yawo da hudubar Juma’ar da Sheikh Abubakar Umar Musa Rijiyar Lemu ya gabatar a ranar Juma’ar da ta gabata.

APC 2023
Limamin Kandahar ya soki malaman da suka goyi bayan APC Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Limamin Kandahar ya tabo malaman musulunci

Kara karanta wannan

Yadda zanga zangar lumana ta zama silar barna da lalata dukiyoyin miliyoyi a Kano

A Facebook Anwar Ahmad Chedi ya gutsuro bangaren hudubar inda aka ji limamin ya maida hankali a kan wasu abokan aikinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Limamin masallacin na Abdullahi Ibn Abbas da ke unguwar Rijiyar Lemu ya yi Allah-wadai ne da dabi’ar wasu malaman musuluncin.

Hudubar ta shafi halin da kasa ta ke ciki ganin yadda matasa su ka fito zanga-zangar lumanar da ta rikida ta zama tashin tashina.

A hudubar da ya gabatar a masallacin da ke Rijiyar Lemu a Kano, ya daura kason laifi a kan malaman da suka tallata APC a 2023.

Ana zargin wasu malaman musulunci su ka fito da karfinsu wajen ganin an zabi Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaben bara.

Kamar yadda aka ji a bidiyo, malamin ya ce dole talakawa su san ciwon kansu, su daina yin zabe saboda sun karbi abin duniya.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi ya bayyana mummunar illar da zanga zanga ta jawo a Kano da Arewa

"Malamai sun zama mutanen banza" - Kandahar

"Wanene zai kawo gudumuwa, zai kawo agaji, zai taimaka, zai kawo dauki da gyara ga al’umma? Shi ya kamata a zaba."
"Ba kowane awon igiya ya zo shikenan ba. A nan su ma wasu da yawa daga cikin wadansu malamai sun zama mutanen banza da wofi."
"Sun fito wai muslim-muslim bayan karya su ke yi, babu wani muslim-muslim, an zo an saye ku saboda abin da za ku lasa."
"Saboda talaucin zuciya kun zo ku na wani muslim-muslim, shiyasa idan kun je gaban shugaban kasar, ba ya ganin kimarku saboda kun zama leburorinsu."

- Sheikh Abubakar Umar Musa Rijiyar Lemu

Zaman malamai da shugaba Bola Tinubu

A karshen gabar, ya ce malaman da aka saya da kudi da zabe sun zama mutanen banza.

Da malamai su ka zauna da shugaban kasa, Sheikh Kandahar ya ce ba su iya yi masa fada ba, a karshe shi ne ya yi masu fada a Aso Rock.

Kara karanta wannan

Limamin Juma’a ya turawa Tinubu da sauran shugabanni sako mai ban tsoro a huduba

Aisar Fagge a shafinsa ya ce malamin ya tabo iyayen da suka bari yarensu su ka saci kayan al’umma da sunan zanga-zangar lumana.

"Dole mu faɗawa kanmu gaskiya ko da ba ma son ji."

- Aisar Fagge

Hudubar Limamin ITN a ranar Juma'a

An rahoto babban malamin musuluncin nan, Ahmad Bello Dogarawa ya yi kira ga duka shugabannin da ke mulki a hudubar ranar Juma’a

A hudubar da ya gabatar a masallacin ITN, Farfesa Ahmad Bello Dogarawa ya yi kira ga masu mulki da shugabannin hukumomi da kuma talakawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng