Sojoji Sun ‘Fatattaki’ Mutane Daga Teburin Shayi, Ana Zargin Sun Kwashe Burodi da Madara

Sojoji Sun ‘Fatattaki’ Mutane Daga Teburin Shayi, Ana Zargin Sun Kwashe Burodi da Madara

  • Magaji Kabiru Getso ya zargi jami’an tsaro da shigowa unguwarsu domin tabbatar da dokar zaman gida a Kano
  • A cewarsa matashin da yake yi wa kan shi lakabi da Al-Getsowi, sojoji sun wawushi kaya daga teburin mai shayi
  • Duk da labarin bai tabbata ba, ya karade wurare da yawa a unguwar Dorayi da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Wani mai suna Magaji Kabiru Getso ya zargi dakarun sojojin kasar Najeriya da yi masu aika-aika a lokacin zanga-zanga.

Malam Magaji Kabiru Getso ya yi magana a shafin Facebook ya na mai zargin sojoji da amfani da damar dokar kulle a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yadda zanga zangar lumana ta zama silar barna da lalata dukiyoyin miliyoyi a Kano

Sojoji
An zargi Sojoji da yin barna lokacin zanga-zanga a jihar Kano Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kano: Dakarun Sojoji sun shiga Dorayi

A cewarsa, sojoji sun rutsa mutane a unguwarsu a safiyar Juma’a, 2 ga watan Agusta 2024 lokacin da aka haramta walwala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a teburin wani mai shayi da ke unguwar Dorayi a karamar hukumar Gwale da ke tsakiyar birnin Kanon dabo.

Bayan sun kori mutane zuwa gida, Magaji Kabiru Getso ya yi ikirarin sojojin sun yi amfani da damar sun cinye masa burodi da madara.

“Yanzu-Yanzu a Unguwarmu Ɗorayi, Sojoji sun tarwatsa mutane a wajen Mai shayi sun kwashe masa Bread da madara"

- Magaji Kabiru Getso

Da gaske sojoji sun dura teburin shayi?

Mutane da-dama su ka rika maida martani a dandalin na Facebook tun a safiyar ranar.

Jama’a sun tambaya ko da gaske abin ya faru, shi kuwa Magaji Kabiru Getso ya tabbatar masu da gaske cewa hakan ta faru ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Dalilin shigata zanga zangar lumana a Kano Inji tsoho mai shekaru kusan 70 a suniya

Magaji Getso ya rantse masu da Allah SWT cewa an wawushe kayan mai shagon shayin.

Haka labarin yake yawo a Dorayi - Kano

Legit Hausa ta tuntubi wani mazaunin Dorayi a Kano domin jin gaskiyar labarin da ya ke yawo a dandalin sada zumuntan tun a jiya.

Musa Abba Gana ya shaida mana cewa ya ji ana labarin tun ranar Juma’a, amma bai da tabbacin yadda ko kuwa inda abin ya faru.

Mazaunin ya shaida mana su na gida saboda dokar kulle, ya kuma kara da cewa ‘yan daba sun shigo unguwar sun sari mutane a dazu.

Dattijo ya koka da halin da ake ciki

Bashir Alhassan haifaffen Dorayi ne, a hirarsa da Legit Hausa ya zargi gwamnatocin tarayya da jihohi da kara jefa kowa a wahala a yau.

“Kananan hukumomi sun fi kusa da talaka, amma ka na ganin yanzu ba su da wani amfani, tamkar babu su.”

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi ya bayyana mummunar illar da zanga zanga ta jawo a Kano da Arewa

“Gwamnoni sun danne su sannan ba su iya yin abin da su ke yi a baya. Garin gwamna ba karamin garari ba ne.”

- Bashir Alhassan

Zanga-zangar lumana da aka yi a Kano

Rahoto ya zo cewa matsin rayuwa da aka shiga ya jawo dole mutane su ka hau titi, a karshe miyagu su ka buge da yin barna a garin Kano.

Bata-gari sun yi barna sosai a Kano, an fasa shagon har da wani mai goyon bayan zanga-zangar lumana kafin abin ya faru a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng