Yadda Zanga Zangar Lumana Ta Zama Silar Barna da Lalata Dukiyoyin Miliyoyi a Kano
Kano - A maimakon a shirya zanga-zangar lumana a ranar 1 ga watan Agusta 2024, sai aka ji bata-gari su na barna a wasu wurare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
A cikin garuruwan da wannan ta’adi ya fi fitowa fili akwai Kano, inda aka ga bidiyon matasa su na satar dukiyar gwamnati da al’umma.
Saboda abin da ya faru ne gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sa dokar hana fita a jihar Kano.
Zanga-zangar lumana ko barna?
A sakamakon barnar da ka yi, Daily Trust ta rahoto cewa wasu ‘yan kasuwa su na kwance a asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun zo cewa an yi barna a titin Zoo Road da Zariya Road da ke birnin Kano, ana ji ana gani miyagu suka rika fasa shaguna.
Legit Hausa ta fahimci cewa tun cikin daren ranar da za a fara zanga-zangar, wasu miyagu su ka fasa shagon Rufaidah Yoghurt a Hotoro.
Washegari kuma an ji cewa an tarwatsa wani shagon na Rufaidah Yogurt a Rijiyar Lemu inda ake saida madara da sauran kayan kwalama.
Ana zargin APC da bata zanga-zanga
Rahoton Sahara Reporters ya ce ana zargin akwai hannun 'yan adawa wajen wannan ta'adi yayin da ake zargin jami'an tsaro da kauda kai.
Hotunan magoya bayan APC su na yawo da sunan cewa sun jawo hargitsi a ranar Alhamis, Arise ta ce jam'iyyar tana zargin NNPP da barnar.
Alhaji Abdullahi Abbas da Rabi’u Sulaiman Bichi sun fitar da jawabi da ya nuna babu hannun APC da magoya bayan tsohon Sarki a rikicin.
A wani bidiyo a Facebook, ana zargin an ga wani babba a APC ya tara jama'a gabanin zanga-zangar, ya na ba da umarnin yadda za su fita.
Zanga-zanga ya jawowa IG Wala asara
Ibrahim Garba Wala, 'dan gwagwarmaya da aka fi sani da IG Wala yana cikin wadanda su ke kokarin karbowa talakawa ‘yancinsu a Najeriya.
A zanga-zangar da aka yi, aka fasa shagon kamfaninsa, ShawaliNG, aka sace kayan ciki tun daga na’urori, kayan aiki zuwa tagogi da kofofi.
‘Dan gwagwarmayan ya ba masu zanga-zangar lumana kariya a shafin Facebook, yake cewa bata-garin da ke bangar siyasa ne suka yi aika-aikar.
“Masu zanga zangar neman mafita sun wuce kimar yin barna ko satar. Matasan da 'yan siyasa ke turasu suyi satar akwatin zabe ne sukayi barna da satar.”
- IG Wala
Dr. Aliyu Isa Aliyu ya koka tun a ranar, ya ce bata-gari sun yi amfani da damar zanga-zangar, sun sace kaya a shagon wata ‘yar uwarsa a Kano.
Malamin jami’ar yana cikin manya a gwamnatin Kano da NNPP, ya ce an dura shagon da ake saida kayan daki, an yi gaba da dukiyar miliyoyi.
Har kayan gwamnati ba su tsira ba, an ga yadda matasa su ka aukawa wani ginin NCC, su ka rika awon gaba da kayan aiki da na’urori.
Gurabattun matasan sun bi tituna sun sace fitulu sun kona motoci a sakatariya da asibiti.
Zanga-zanga: An yi ta'adi a ofishin NCC
Yakubu Musa ya yi magana a Facebook, ya ce miyagun sun yi ta’adin ne a lokacin da ake shirin kaddamar da wurin domin amfanar jama’a.
"An dai karaso Inda ake jin tsoron. A cikin satin nan wuni nake aiki a offfice don za a bude wannan katafaran gini na ‘Digital Industrial Park’ da aka kawo Kano a cikin sati mai zuwa. Shi kadai ne duk fadin Arewa maso Yamma wanda gaba daya shida ne a Nigeria.”
“An samar da shi don ilmantar da matasa da kuma kyankyasar sabbin zakakurai ta bangaran kirkirar fasaha. Yanzu ga shi an yi masa wasoso and sace muhimman naurori tare da gagarumar barna. Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.”
- Yakubu Musa
Ina 'yan sanda da ake zanga-zanga?
Ana zargin 'yan sanda sun kyale mutane sun ci karensu babu babbaka da ake zanga-zangar, dama can akwai sabani tsakansu da gwamnati.
Gidan rediyon Freedom ta rahoto jami'an tsaron su na yabawa gwamna kan matakin da ya dauka sai dai hakan bai kauda wannan zargi ba.
Ibrahim Adam ya ce an sanar da 'yan sanda akwai masu shirin kai hari a mada'abar gwamnatin Kano, amma ba ta dauki mataki ba.
Legit ta yi hira da wasu, ta ji yadda jami’an ‘yan sanda suka dage wajen hana bata-gari aukawa shagon Garba karfe a unguwar Na’ibawa.
Dakarun ‘yan sanda sun bukaci masu zanga-zanga su koma tsallaken titi domin gudun a fasa babban shagon, a jawo asarar dinbin dukiyoyi.
Wasu shaguna irinsu Barakat Store ba su tsira ba, an sace kayan abinci da makamantansu duk da ana kokarin tono inda aka kai kayayyakin.
Abin farin cikin shi ne an ji labari jami’an tsaro sun fara gano wasu kayan da aka sace a ranar Alhamis kuma an damke wasu da ake tuhuma da laifi.
Zanga-zangar masoyan Tinubu a Kano
Yayin da Najeriya ta rikice da zanga-zanga, an ji labari wasu masoyan shugaban kasa, Bola Tinubu sun yi tattakin goyon baya a makon jiya.
A jihar Kano, magoya bayan Tinubu sun bayyana cewa a yi hakuri a ba wa shugaban kasa lokaci wajen tabbatar da gyaran da yake nufin yi.
Wadannan mutane sun tabbatar da cewa da gaske akwai tsanani a Najeriya, amma shugaban kasa lokaci ya ke bukata ba a hau kan tituna ba.
Asali: Legit.ng