Cigaba 6 da Aka Samu da ba a Maganarsu Bayan Tinubu Ya Karbi Mulki a Hannun Buhari
Abuja - Daga lokacin da aka ce Bola Ahmed Tinubu ya karbi mulki, an yi ta kokarin kawo sauyi a bangaren tattalin arziki a kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Duk da mafi yawan jama’a su na kuka da tsadar rayuwa, hauhawar farashi da tashin kudin fetur, akwai wasu nasarorin da aka samu.
Kwanakin baya Olusegun Dada, ya jero wasu cigaba a X da aka samu a tattalin arziki cikin shekara guda da shugaban kasar ya yi a ofis.
Mista Olusegun Dada yana cikin masu taimakawa Bola Tinubu a kafofin sada zumunta. Hadimin shugaban Najeriyan ya jero abubuwa 6:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasarorin Bola Tinubu a fannin tattalin arziki
1. Asusun kudin kasar waje
Daga $33.09bn a karshen shekarar 2023, alkaluman babban bankin CBN sun nuna asusun kudin kasar wajen Najeriya ya karu a yanzu.
A cewar Dada, kudin kasar wajen ya kai $35.05bn a watan Yulin nan. The Nation ta ce zuwa yanzu kudin cikin asusun ya zarce $35.77bn.
2. Karin albashi
A yayin da Bola Tinubu ya hau karagar mulki, N30, 000 ne mafi karancin albashin talaka, amma yanzu gwamnati ta maida shi N70, 000.
Wannan kari na sama da 100% bai fara aiki ba tukuna, amma tuni aka sa hannu.
3. Bashin Najeriya
Idan aka kamanta kason bashin da ake bin Najeriya da kudin shiga kafin Yunin 2023, an matukar cigaba a karkashin mulkin Bola Tinubu.
A 2023, kason kudin shiga da bashin da ke wuyan kasar ya kai 97%, yanzu alkaluma sun ce bashi bai wuce 67% na kudin da aka aro ba.
4. Hako danyen mai
Hukumar NUPRC ta ce a yanzu Najeriya tana hako ganguna miliyan 1.61 na danyen mai a kowace rana, kuma za a iya zarce hakan.
Punch ta ce bayanin Injiniya Gbenga Komolafe sun nuna an samu cigaba daga ganguna 900, 000 da ake iya hakowa a watan Mayun 2023.
5. Bashin kudin kasar waje
A watan Mayun 2024, an rahoto Yemi Cardoso ya na cewa bankin CBN ya biya bashin kudin kasar waje da kamfanoni suke bin kasar.
Olayemi Cardoso ya ce biyan wadannan kudi $7.5bn da aka gada zai taimakawa tattali.
6. Bashin cikin gida
Ministan tattalin arziki, Wale Edun ya yi alkawari za a gujewa karbar bashi a hannun CBN kamar yadda Muhammadu Buhari ya rika yi.
A lokacin da aka canza mulki a bara, CBN ta na bin gwamnatin tarayya bashin N26tr da aka buga mata, yanzu bashin kudin ya koma N16tr.
Kira ga Tinubu da gwamnoni a jihohi
A baya an kawo rahoto cewa Farfesa Ahmad Bello Dogarawa ya yi kira ga duka shugabannin da ke mulki a hudubar ranar Juma’ar nan a Zariya.
Babban malamin musuluncin ya yi kira ga masu mulki da shugabannin hukumomi da kuma talakawa su ji tsoron Allah a duka al'amuransu.
A hudubar da ya gabatar, limamin ya ce duk shugaban da bai yi adalci ba, ba zai ji kanshin aljannah ba idan an tafi filin kiyama a gobe lahira.
Asali: Legit.ng