Limamin Juma’a Ya Turawa Tinubu da Sauran Shugabanni Sako Mai Ban Tsoro a Huduba

Limamin Juma’a Ya Turawa Tinubu da Sauran Shugabanni Sako Mai Ban Tsoro a Huduba

  • Farfesa Ahmad Bello Dogarawa ya yi huduba a masallacin ITN a Zariya, inda ya yi kira ga masu mulki a Najeriya
  • Limamin ya tunawa shugaban kasa da gwamnoni ayoyin Kur’ani da wasu daga cikin hadizin Manzon Allah SAW
  • Sheikh Dogarawa ya yi nasiha a kan zanga-zangar lumanar da ake yi wanda ta rikide zuwa tashin tarzoma a jihohi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Farfesa Ahmad Bello Dogarawa ya yi hudubar Juma’a a jiya inda ya yi magana musamman a kan halin rayuwa a yau.

Malamin jami’ar ta Ahmadu Bello da ke Zariya ya maida hankali ne a kan zanga-zangar da aka shirya wanda ta zama fitina a wurare.

Kara karanta wannan

Dalilin shigata zanga zangar lumana a Kano Inji tsoho mai shekaru kusan 70 a suniya

Bola Tinubu
An yi kira ga Bola Tinubu da Gwamnonin Najeriya a hudubar Juma’a Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Legit Hausa ta saurari hudubar Ahmad Bello Dogarawa a ranar 27 ga watan Muharram 1446 a Facebook, inda aka ji ya yi nasiga ga jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Limami ya yi magana kan zanga-zanga

Malamin yake cewa tabbas jama’a su na cikin kuncin rayuwa, saboda haka ne wasu su ka yi tunanin shirya zanga-zangar lumana.

Farfesa Ahmad Dogarawa ya ce dole ayi hattara da fitinar da za ta iya shafan wadanda suka tsokano ta da wadanda babu hannunsu.

Kira ga Tinubu da sauran shugabanni

A hudubar da ya yi a masallacin ITN da ke garin Zariya, limamin ya tunawa shugabanni cewa dole su yi adalci wajen jagorancinsu.

Idan har ba a kamanta gaskiya, malamin ya ce za a samu wasu mutane da za su ware, su rika jin cewa sun zama bare cikin al’umma.

Idan aka samu wasu daidaiku da suka fandare, hakan yana haifar da tashin-tashina, su nemi dama irinta zanga-zanga wajen yin ta’adi.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi ya bayyana mummunar illar da zanga zanga ta jawo a Kano da Arewa

Hudunar ta kawo maganganun malaman musulunci irinsu Ibn Taimiyyah da Imam Mawardy da suka yi rubutu a kan mulki a musulunci.

Idan ana so daula ta daure, wajibi ne masu mulki su kula da addinin al’umma, adalci, shugabanci na gari, tsaro da hangen nesa.

Shehin yake cewa bai halatta wani shugaba ya kasafta dukiyar al’umma yadda ya ga dama, dole ya yi adalci tsakanin talakawansa.

"Tinubu ku ji tsoron Allah SWT"

Marubucin ya yi kira ga shugaban kasa da gwamnoni su ji tsoron Allah a kan alamar da ke kan su da nauyin da suka dauka a 2023.

"Ko shakka babu, wajibi ne su tuna cewa Allah madaukin Sarki zai tambaye su a ranar kiyama."

- Farfesa Ahmad Bello Dogarawa

A hudubar, limamin ya ambaci hadisin da Manzon Allah ya yi addu’a mai zafi a kan shugabannin da suka kuntatawa mutanensu.

Hudubar ta tunawa masu mulki cewa duk wanda bai yi adalci ba, ba zai ji kanshin aljanna ba.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yi magana yayin da zanga zanga ta ƙara ɓarkewa a Kano

Shugaba Tinubu ya nada mukami

A can baya aka rahoto cewa Shugaban kasa ya yi sabon nadi ga Ajuri Ngelale wanda mai ba shi shawara ne a kan harkokin yada labarai.

Bola Ahmed Tinubu ya yi nadin ne ta hannun Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume wanda ya sanar a birnin Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng