‘Dan Majalisar NNPP Ya Gargadi Hon Alhassan Doguwa kan Taba Kwankwaso a Kano
- Abdulmumin Jibrin Kofa bai ji dadin yadda ‘dan majalisar Tudun Wada/Doguwa ya caccaki madugun Kwankwasiyya ba
- ‘Dan majalisar Kiru da Bebeji ya yi wa Hon. Alhassan Ado Doguwa kashedi da kyau, ya nuna za su iya daukar mataki a kan shi
- Doguwa ya caccaki Kwankwaso kwanaki, Hon. Jibrin ya tunawa ‘dan siyasar cewa jagoran Kwankwasiyya ba sa’an shi ba ne
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Jano – Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa mai wakiltar Kiru da Bebeji ya ja kunnen abokin aikinsa a majalisar tarayya, Hon. Alhassan Ado Doguwa.
Abdulmumin Jibrin Kofa ya gargadi Alhassan Ado Doguwa wanda yake wakiltar Tudun Wada/Doguwa ya daina taba Rabiu Musa Kwankwaso.
Sakon Abdulmumin Jibrin ga Ado Doguwa
A wani jawabi da Sani Ibrahim Paki ya fitar a shafin Facebook, an ji ‘dan majalisar wakilan tarayyan yana ba da kariya ga Rabiu Musa Kwankwaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan siyasar ya fadawa Alhassan Doguwa cewa madugun darikar Kwankwasiyya kuma tsohon Gwamna, Rabiu Kwankwaso ba sa’an shi ba ne.
Abdulmumin Jibrin ya tallafawa mazabarsa a Kano
Abdulmumin Jibrin ya bayyana wannan ne a lokacin wani gangami inda ya hadu da mutane 5, 000 daga cikin magoya bayansa a mazabarsa.
Hon. Jibrin ya yi amfani da damar wajen rabon takin zamani da fam domin karbar tallafin N150, 000.
Gidaje 1, 000 za su amfana da tallafin ‘dan majalisar wannan karo, sannan an rahoto cewa zai raba fitulun kan titi 200 domin haskaka gari.
Shugaban kwamitin harkokin gidaje a majalisar tarayyar zai kuma raba takardun ayyuka ga wasu daga cikin ‘yan mazabarsa a Kano.
A wurin ya yi amfani da damar ya aika sakon jan kunne ga Alhassan Ado Doguwa, ya ce idan bai yi hattara ba, dole za su dauki mataki a kan shi.
Abdulmumin Jibrin ya kare Rabiu Kwankwaso
"Ina so in gargadi Alhassan Ado Doguwa ya daina taba jagoranmu, Senator Rabiu Musa Kwankwaso domin mu na girmama shi kuma mu na Daraja shi a matsayin abin koyi, jagora kuma uba."
"Ba mu taba jagororinsu, saboda haka su daina taba ba mu."
Wannan martini ne ga sukar Kwankwaso da Hon. Doguwa ya yi kwanakin baya, Jibrin ya ce Kwankwaso ya yi masa nisa sosai a siyasa.
Duk da sun je majalisa tare da jagoransu a 1992, Jibrin ya ce Kwankwaso ya yi aikin gwamnati, ya yi gwamna, Minista da Sanata.
Kwankwaso ya ce a guji zanga-zanga
A makon jiya an ji labari Rabiu Kwankwaso ya roƙi masu shirya zanga-zanga su duba sakamakon da zai biyo baya na asarar rayuka da dukiyoyi.
Jagoran NNPP na ƙasa ya roƙi ƴan Najeriya su yi amfani da ƙarfin kurinsu wajen sauya duk shugaban da ya yi masu ba daidai ba idan an je filin zabe.
Asali: Legit.ng