Zanga Zanga: Matasa Sun Nuna Turjiya Bayan An Yi Musu Ruwan Borkonon Tsohuwa

Zanga Zanga: Matasa Sun Nuna Turjiya Bayan An Yi Musu Ruwan Borkonon Tsohuwa

  • A yau Juma'a matasa suka shiga rana ta biyu domin gudanar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a dukkan jihohin Najeriya
  • Duk da cewa wasu jihohin an saka dokar hana zirga zirga, dandazon matasan Najeriya sun fito zanga zanga a birnin tarayya Abuja
  • Daya daga cikin jagororin zanga zangar a birnin Abuja ya koka kan yadda yan sanda suka rika ta'azzara musu yayin da suka fito

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jagorin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya sun koka kan rashin samun hadin kan jami'an tsaro a Abuja.

Kungiyar Take It Back Movement ta yi ikirarin cewa yan sanda sun muzgunawa wasu masu zanga zanga a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An kashe mutane 14, an kama 'Yan Shi'a cikin wadanda ake zargi da laifi

Zanga zanga
Masu zanga zanga sun koka a Abuja. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban hada kan jama'a na kungiyar, Damilare Adenola ne ya yi bayani a yau Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An harba borkonon tsohuwa ga matasa

Damilare Adenola ya ce a safiyar yau Jumu'a yan sanda suka rika fesa musu borkonon tsohuwa a birnin tarayya Abuja amma ba duk da haka sun cigaba da zanga zangar.

Jagoran zanga zangar ya ce matasan sun taru ne a daidai shatale-talen Berger da ke cikin birnin tarayya domin cigaba da zanga zanga.

Adenola: 'Tinubu ya gaza kare dimokuraɗiyya'

Shugaban zanga zangar ya ce muzgunawa matasa a filin zanga zanga na nuni da cewa gwamnatin tarayya ba ta girmama dimokuraɗiyya.

Damilare Adenola ya ce ya fadi haka ne saboda kasancewar dimokuraɗiyya ce ta ba matasan Najeriya yancin yin zanga zangar lumana.

Zanga-zanga: Adenola ya ji tsoron tunzura matasa

Har ila yau, Damilare Adenola ya ce akwai abin tsoro wajen rashin samun hadin kan jami'an tsaro a lokacin zanga zangar.

Kara karanta wannan

Kwana 1 da zanga zanga, gwamnatin Tinubu ta bude kofa kan bukatun talakawa

Ya ce idan suka cigaba da muzgunawa matasa hakan zai sa su kara tunzura wanda dama rayukansu a bace suke.

Abuja: An nemi sulhu da masu zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi magana a karon farko bayan matasan Najeriya sun fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ne ya yi kira ga matasan Najeriya domin neman hanyar kawo karshen zanga zangar baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng