Zanga Zanga: An Kashe Mutane 14, An Kama 'Yan Shi'a Cikin Wadanda Ake Zargi da Laifi
- Zanga zangar da matasa suka fara gudanarwa a Najeriya kan tsadar rayuwa ta jawo asarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa
- An ruwaito cewa an kashe mutane da dama a jihohin Kaduna, Borno, Neja da sauransu ciki har da jami'an tsaro yayin zanga zangar
- Rundunar yan sanda ta kama mutane da dama da ake zargi da aikata laifuffuka da dama a sassan Najeriya yayin zanga zangar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya ta jawo asarar rayuka da dukiya mai yawa a ranar farko.
Rahotanni sun nuna cewa zanga zangar ta rikide ta koma tarzoma a jihohi da dama musamman a Arewacin Najeriya.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa rundunar yan sanda ta yi nasarar cafke da dama daga cikin wadanda suka fara sace sace a lokacin zanga zangar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe mutane 14 a zanga zanga
A ranar farko ta zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya an kashe mutane akalla 14 a sassan Najeriya, musamman a Arewa.
A jihar Neja, an kashe mutane shida a yankin Suleja yayin da aka kashe mutane hudu a gidan mai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Haka zalika an kashe mutane uku a jihar Kaduna, sannan aka kashe wani dan kasuwa a shagonsa a Yauri da ke jihar Kebbi.
Zanga zanga: An zargi yan Shi'a da tarzoma
Kakakin rundunar yan sanda a jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan ya zargi yan Shi'a da mayar da zanga zangar lumana tarzoma a Kaduna.
ASP Mansir Hassan ya ce an fara zanga zangar lami lafiya kafin su shigo su fara tayar da hankali daga nan kuma lamari ya rikice a jihar.
Rahoton Channels Television ya nuna cewa rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta yi nasarar cafke mutane 25 da ake zargi da yin sace sace a lokacin zanga zangar.
Matasa sun yi rikici da yan sanda
A wani rahoton, kun ji cewa matasan Najeriya suka cika titunan domin yin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a kusan dukkan jihohin kasar.
A jihar Kaduna an samu rashin jituwa tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zanga inda har lamarin ya kai ga yin harbi sama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng