“An Kashe Dan Sanda”: IGP ya ba Jami’an Tsaro Sabon Umarni Kan Masu Zanga Zanga

“An Kashe Dan Sanda”: IGP ya ba Jami’an Tsaro Sabon Umarni Kan Masu Zanga Zanga

  • Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya mayar da martani kan zanga-zangar da aka gudanar a fadin kasar a ranar Alhamis
  • Da yake magana a wani taron manema labarai, IGP Egbetokun ya ce an kashe jami'i guda yayin da wasu jami’an suka samu raunuka
  • Bisa la’akari da halin da ake ciki yanzu, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanya dukkanin rundunonin tsaro cikin shirin ko-ta-kwana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun ya ce an kashe dan sanda a lokacin da yake bakin aiki a yayin zanga-zangar yunwa a ranar Alhamis.

A taron manema labarai da aka yi a Abuja, shugaban ‘yan sandan ya ce 'yan daba da suka saje cikin masu zanga-zangar sun raunata jami'ansa da dama.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun kona ofishin 'yan sandan Abuja? An samu cikakken bayani

Sufeta Janar (IGP) Kayode Egbetokun ya yi magana kan barnar da masu zanga zanga suka yi
Rundunar 'yan sanda ta ce masu zanga-zanga sun kashe jami'inta 1 da lalata ofisoshi. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

"Yan daba sun kwace zanga-zanga" - IGP

IGP Egbetokun ya ce fusatattun matasan da suka juyar da zanga-zangar zuwa tashin hankali sun lalata wasu ofisoshin ‘yan sanda a sassan kasar, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban 'yan sandan ya koka da cewa abubuwan da suka faru a manyan biranen kasar a ranar alhamis "tashin hankali ne da satar dukiya, ba zanga-zanga ba".

Masu shirya zanga-zangar dai ba su ne suka jagoranci gangamin ba duk da gargadin farko da ‘yan sanda suka yi, ya kuma kara da cewa ‘yan daba ne suka mamaye zanga-zangar.

Masu zanga-zanga sun kashe dan sanda

Jaridar Daily Trust ta ruwaito IGP Egbetokun na cewa:

“An lalata ofisoshin ‘yan sanda. An yi yunkurin mamayewa tare da kwace ikon gidajen gwamnati.
“A wurare irinsu Abuja Kaduna, Kano da Gombe da dai sauransu, an kai hare-haren ba gaira ba dalili kan jami'anmu inda aka kashe dan sanda guda tare da jikkata wasu.

Kara karanta wannan

"Jami'an tsaro sun gano sanata mai daukar nauyin zanga zanga," Minista Wike ya yi magana

“Bisa la’akari da halin da ake ciki yanzu, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanya dukkan rundunonin tsaro cikin shirin ko-ta-kwana.

Sufetan 'yan sandan kasar ya ce jami'an rundunar sun yi cikakken shiri kuma suna jiran umarni domin mayar da martani a shirin tabbatar da tsaron al'umma da dawo da tsaro.

An kashe mutane daga zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa an kashe wasu matasa guda hudu a lokaci daya a wani gidan mai gidan man Kime da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta ce harsashin bindiga ne ya samu matasan inda suka mutu nan take, kuma har lokacin gawarsu na a gidan man.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.