Jihohin Arewa da Aka Sanya Dokar Hana Fita ta Awa 24 Sun Kai 4, an Samu Cikakken Bayani
A safiyar yau Alhamis, 1 ga watan Agustan 2024 ne aka fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin Najeriya, lamarin da ya rikide zuwa tashin hankali a wasu jihohi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A yayin da wadanda suka shirya zanga-zangar su ka ce za ta kasance ta lumana ne, a lokacin ne kuma rahotannin kashe kashe, lalata kadarori da satar dukiya ke kara yaduwa.
Sakamakon tashe tashen hankula da wannan zanga-zangar ta haifar, akwai wasu gwamnonin Arewa guda uku da suka sanya dokar hana fita ta awanni 24.
An sanya dokar hana fita a Yobe
Gwamna Mai Bala Buni na jihar Yobe ya sanya dokar hana fita ta awa 24 bayan gwamnati ta gano 'yan daba sun kwace zanga-zangar yunwa a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mun ruwaito cewa mai ba gwamnan Yobe shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdussallam (mai ritaya) ya sanar da sanya dokar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce dokar ta shafi garuruwan Potiskum, Gashua da Nguru na jihar inda aka gano 'yan dabar na shirin lalata dukiyar jama'a.
Abba ya sanya doka a Kano
A jihar Kano kuwa, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya dokar hana yawo saboda tashe tashen hankula da suka faru ana tsaka da zanga-zanga.
Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a gidan gwamnatin jihar wanda hadiminsa, Abdullahi Ibrahim ya wallafa a shafin X.
Sanarwar ta ce an sanya dokar hana fita ta awa 24 a fadin jihar Kano kuma gwamnan ya ba jami'an tsaro umarnin daukar mataki kan wadanda suka karya ta.
An sanya dokar hana fita a Borno
Legit Hausa ta rahoto gwamnatin jihar Borno ce ta fara sanya dokar hana fita ta awanni 24 bayan da wani bam ya tashi a a kasuwar Kawori da ke yankin Konduga a jihar Borno.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta yi nuni da cewa fashewar bam ne ya sa Gwamna Babagana Zulum ya tuntubi manyan jami’an tsaro kafin aiwatar da wannan matakin.
Katsina: Mukaddashin gwamna ya sanya doka
A Katsina, mukaddashin dwamnan jihar, Malam Faruq Lawal, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Dutsin-Ma.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito mukaddashin gwamnan ya kuma sanar da sanya dokar hana fita daga karfe 7 na dare zuwa 7 na safe a sauran kananan hukumomin 33.
Ya kuma haramta duk wata zanga-zanga a fadin jihar, inda ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Legit Hausa ta ji ta bakin Mallam Nura
A zantawarmu da Nura Haruna Maikarfe daga karamar hukumar Funtua, ya shaida mana cewa wannan dokar da aka sanya za ta taimaka wajen magance matsalar tsaro.
A cewar Nura Haruna, dama bai kamata a yi wannan zanga-zangar a jihohin Arewa maso Yamma ba inda aka san suna fama da matsalar tsaro ta 'yan bindiga.
Mai sharhi kan lamuran jihar ya yi kira ga al'ummar yankin da suka fi fuskantar matsalar tsaro da su yi biyayya ga wannan dokar domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.
An kashe mutum 1 a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa an kashe mutum daya yayin da masu zanga-zanga suka kona ofishin hukumar NCC, gidan mai da wasu gine gine a jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe matashin mai suna Ismael Ahmad Musa a yankin Hotoro da ke karamar hukumar Tarauni a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng