Yadda Matasa Suka Daƙile Yunkurin Ministan Tinubu a Filin Zanga Zanga
- Matasan a sassan kasar nan sun wuni suna gabatar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a kusan dukkan jihohin Najeriya
- Haka zalika a birnin tarayya Abuja, matasa da dama sun fita zanga zangar adawa da tsadar rayuwa inda suka yi kira ga Bola Tinubu
- Karamin ministan matasa, Ayodele Olawande ya ziyarci dandalin Eagle Square inda matasan suka daƙile shi daga magana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Matasan Najeriya sun yi taru a dandalin Eagle Square a Abuja domin yin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.
Karamin ministan matasa, Ayodele Olawande ya ziyarci dandalin domin yin bayani amma bai samu dama ba.
Jaridar Punch ta wallafa cewa ministan ya lallabi matasan domin ya shawo kansu amma abin ya gagara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda matasa suka hana minista magana
A yayin da karamin ministan matasa, Ayodele Olawande ya isa wajen masu zanga zanga a dandalin Eagle Square ya yi niyyar masu magana.
Amma sai matasan suka daƙile shi wajen yin ihun cewa suna jin yunwa wanda hakan yasa bai samu hadin kansu a dandalin ba.
Ministan Tinubu ya yi magana daga baya?
Bayan dandazon jama'a ya ragu a dandalin, Ayodele Olawande ya samu damar yin magana da wasu matasan.
Ministan ya ce ba ya je dandalin ba ne domin ya hana su yin zanga zangar lumana sai dai ma ya ce zanga zanga na cikin hakkin yan kasa.
'Nima na yi zanga zanga' - Ministan matasa
Karamin ministan tarayyar, Ayodele Olawande ya tabbatarwa matasan cewa shi ma ya yi zanga zanga a baya sosai.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Ayodele Olawande ya bayyana cewa akalla ya halarci zanga zanga guda kusan 100 ko 500 a tsawon rayuwarsa.
Malami ya shiga zanga zanga a Jos
A wani rahoton, kun ji cewa a yau ne al'ummar Najeriya suka fito kan tituna a faɗin ƙasar nan domin gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa.
Wani fitaccen malamin addini a jihar Filato, Dakta Isa El-Buba ya jagoranci matasa domin gudanar da zanga zangar a birnin Jos.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng