Zanga Zanga: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Gano Dalilin Tashin Hankali A Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya dora alhakin rikidewar zanga-zanga zuwa tashin hankali a Kano a kan wasu marasa kishin jihar
- Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da masu zanga-zanga a jihar bayan an samu rahotannin jiwa 'yan sanda rauni
- Gwamnan ya ce an dauko hayar wasu bata-gari mota-mota zuwa jihar Kano a safiyar yau, inda su kuma su ka fara tayar da hatsaniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaicin yadda marasa kishin jihar Kano su ka shiga cikin masu gudanar da zanga-zanga wajen tayar da hankula.
An tabbatar da rasuwar mutum guda a jihar yayin da matasa su ka rika fasa gidajen kayan abinci da shaguna har da jiya 'yan jarida rauni a yau Alhamis.
A jawabin gwamnan da Freedom radio ta wallafa kai tsaye a shafinta na Facebook, Abba Kabir Yusuf ya ce sun cimma matsayar tabbatar da zanga-zangar lumana a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marasa kishin Kano sun shigo zanga-zanga
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya dauki alkawarin sauraren koken masu zanga-zanga a jihar domin mikasu ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
A sakon da ya tura ga masu zanga-zangar a safiyar yau a gidan gwamnatin Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce tuni matasan su ka tabbatar da cewa ba za su tayar da hatsaniya ba.
Ya ce dukkanin 'yan kasa su na da 'yancin bayyanawa mahukunta bacin ransu, kamar yadda Premier radio ta wallafa kai tsaye a shafinta na Facebook.
Zanga zanga: An kashe mutum 1 a jihar Kano
A wani labarin kun ji yadda zanga-zangar lumana a Kano ta rikide zuwa tashin hankali wacce ta kai ga kona gidan mai tare da kashe mutum daya a jihar.
Matashin mai suna Ismael Ahmad Musa ya rasu a Hotoro, yayin da wani mutum guda da aka garzaya da shi asibiti bayan harsashi ya same shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng