Zanga Zanga: An Yi Gumurzu Tsakanin Yan Sanda da Matasa a Jihar Arewa

Zanga Zanga: An Yi Gumurzu Tsakanin Yan Sanda da Matasa a Jihar Arewa

  • A yau ne matasan Najeriya suka cika titunan domin yin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a kusan dukkan jihohin kasar
  • A jihar Kaduna an samu rashin jituwa tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zanga inda har lamarin ya kai ga yin harbi sama
  • Matasa masu zanga zangar tsadar rayuwa a Kaduna sun rufe hanyar da ta haɗa jihohin Kano da Kaduna inda matafiya suka carke

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - An samu sabani tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Kaduna.

Jami'an tsaro sun yi kokarin korar masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa bayan su toshe hanya.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan an bindige masu zanga zanga har lahira a ranar farko

Yan sanda
Yan sanda sun fafata da matasan da suka toshe hanya a Kaduna. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jami'an tsaro sun yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa matasan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa sun toshe hanya a Kaduna

A yayin da matasa ke zanga zanga a kusan dukkan jihohin Najeriya, wasu daga cikinsu sun toshe hanya a Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa matasan sun toshe hanyar kwanar Gwargaje ce wanda hakan ya kawo cunkoso da hana matafiya zuwa Kano.

Yan sanda sun bude hanya a Kaduna

Bayan samun labarin, jami'an yan sanda sun isa wajen inda suka fara lallaɓa matasan kan su bude hanyar amma suka ƙi yarda.

Premium Times ta wallafa cewa biyo bayan haka ne jami'an tsaro suka fesa musu borkonon tsohuwa inda matasan suka gudu daga kan hanyar mutane suka fara wucewa.

Kaduna: Matasa sun kara toshe hanya

Bayan yan sanda sun tarwatsa matasan, sai suka ƙara taruwa suka toshe hanyar kuma hakan ya kara kawo cinkoso.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun ci karfin jami'an tsaro, an toshe babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna

Sai dai an ruwaito cewa jami'an tsaro sun tafi sun kyale matasan suna zanga zanga a kan hanyar ba tare da sun nufi bude ta a karo na biyu ba.

Zanga zanga: An yi kone kone a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa a yau Alhamis, 1 ga watan Agusta aka wayi gari da fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a dukkan jihohin Najeriya.

A Kano, wasu masu zanga zangar sun nufi gidan gwamnati inda suka fara kone konen taya a kofar gidan gwamantin jihar da sanyin safiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng