Masu Zanga Zanga Sun ci Karfin Jami’an Tsaro, An Toshe Babbar Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
- Matasa masu zanga-zangar yunwa sun mamaye babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a daidai kwanar Gauraka da ke a Suleja
- An ce toshe hanyar da matasan suka yi ya jawo cunkoson ababen hawa tun daga kauyen Aluminum har zuwa barikin Zuma
- Wani matafiyi da ya zanta da manema labarai ya ce akwai 'yan sanda a nesa kadan da wajen amma yawan matasan ya fi karfinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja- Daruruwan matafiya ne a halin yanzu suka makale a kan titin Suleja wanda ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a jihar Neja.
Hakan ya faru ne a sakamakon hana zirga-zirgar ababen hawa a wani sashe na hanyar da masu zanga-zangar yunwa suka yi.
Wani mazaunin Abuja, Abubakar Ibrahim, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna, ya shaidawa Daily Trust cewa motar da ya hau ta shafe sama da sa’o’i biyu a waje daya sakamakon rufe hanyar da aka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasa sun toshe hanyar Abuja zuwa Kaduna
A cewar Abubakar:
"Da misalin karfe 10:00 na safiyar yau Alhamis motarmu ta bar garin Zuba inda matasa masu anga-zanga suka toshe hanya a dai dai kwanar Gauraka.
"Mun shafe awanni biyu muna tsaye waje daya, matasan sun mamaye titin gaba daya, kuma an samu cunkoson ababen hawa tsakanin kauyen Aluminum da barikin soji na Zuma."
Wani kokari 'yan sanda suka yi lokacin?
Abubakar Ibrahim ya ce akwai wasu jami'an 'yan sanda da ke nesa kadan da wajen, amma sun gaza yin komai domin nemawa matafiya hanyar wucewa.
"Akwai 'yan sanda kadan da ke tsaye daga nesa, amma ba za su iya yin komai ba game da tsohe hanyar saboda yawan matasan ya fi karfinsu."
- Abubakar Ibrahim
Bauchi: An tarwatsa masu zanga-zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga da suka yi yunkurin mamaye fadar mai martaba sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu.
Tun farko dai masu zanga-zangar sun taru ne a ƙofar fadar Sarkin Bauchi, inda suka nemi a yi masu iso domin su gana da mai martaba sarki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng