Kwanaki 10: Lauya ya Nemi Alfarma, Ya Roki Masu Zanga Zanga su Rage Tsawon Lokaci
- Daga yau, 1 Agusta 2024 ne masu zanga-zanga a Najeriya za su fara fita tituna domin nuna fushinsu a kan kamun ludayin gwamnati
- Masu zanga-zangar sun bayyana aniyar cewa za su gudanar da ita har tsawon kwanaki 10 domin tabbatar da cewa gwamnati ta saurare su
- Amma wani lauya a kasar nan, Ebun Olu Adegboruwa ya roki matasan Najeriya su rage kwanakin da za su gudanar da zanga-zanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Legas - Yayin da ake sa ran fara zanga-zangar gama gari a fadin Najeriya daga yau Alhamis 1-10 Agusta, 2024, an roki matasan kasar nan.
Wani lauya, Ebun Olu Adegboruwa ya ce matasan su yi hakuri, su kuma rage kwanakin zanga-zanga daga kwanaki 10 zuwa kwana ɗaya tal.
Za a rage kwanakin zanga-zanga?
Channels Television ta tattaro cewa lauyan mai matsayin SAN ya yaba da jajircewar matasan Najeriya wajen tabbatar da cewa gwamnati ta ji kukansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma ya yi rokon a rage kwanakin daga 10 zuwa daya ko kwanaki uku zai taimaka sosai wajen ba wa gwamnati damar duba matsalolin da aka zayyana.
"A yi zanga-zanga cikin lumana," Lauya
Babban lauyan a kasar nan, Ebun Olu Adegboruwa ya nemi matasan Najeriya da za su fara zanga-zanga a yau Alhamis da su gudanar da ita cikin lumana.
The Cable ta wallafa cewa dagiyar da rundunar 'yan sanda ta yi na cewa akwai bata-gari da ke son shiga rigar zanga-zanga ya nuna cewa gwamnati na son hana fita.
Ya zargi gwamnati da kokarin dauko 'yan saba da kanta wajen hautsina zanga-zangar, saboda haka ya bukaci matasan su fito cikin lumana da tsari.
Gwamnati ta fadi matsalar zanga-zanga
A baya kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fadi dalilin da ya sa ta nemi matasan kasar nan su hau teburin tattaunawa a maimakon zanga-zanga.
Sakataren gwamnati, George Akume ya bayyana cewa sun hango yiwuwar 'yan Boko Haram da sauran 'yan binga za su shiga cikin masu zanga-zanga domin aika-aika.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng