Tsadar Rayuwa: Jerin Jihohin da Za a Gudanar da Zanga Zanga a Ranar 1 Ga Watan Agusta
- Babban lauya kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya zanga-zangar yunwa ya fitar da wuraren da za a gudanar da zanga-zangar a faɗin Najeriya
- Ebun-Olu Adegboruwa, SAN a wani martani da ya yi wa IGP Kayode Egbetokun, ya lissafo muhimman wurare a jihohi tara daga cikin 36 na ƙasar nan
- Jerin wuraren zai ƙara faɗaɗa kuma wasu jihohi za su iya shiga kamar yadda lauyan ya buƙaci IGP ya ba su ƴan sandan da za su ba su kariya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Ebun-Olu Adegboruwa, SAN, mai wakiltar "Take It Back Movement", ya ba ƴan sanda wuraren da za a gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan.
Adegboruwa ya bayyana sunayen jihohi da wuraren da za a gudanar da zanga-zangar a yayin wani taro da aka yi tsakanin ƴan sanda da wasu zaɓabbun lauyoyin masu shirya zanga-zangar.
A yayin taron, Kayode Egbetokun ya buƙaci a gudanar da zanga-zangar a keɓaɓɓun wurare yayin da masu shirya ta suka haƙiƙance sai sun fito kan tituna, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin jihohin da za a gudanar da zanga-zangar
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, bayan babban sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya buƙaci a bayyana wuraren, Adegboruwa ya samar da wuraren kamar haka:
- Eagles Square, Abuja
- Alausa Park, jihar Legas
- Gidan mai na Rosewale, hanyar Iwo, Ibadan, jihar Oyo
- Freedom Park, Oshogbo, jihar Osun
- Kusa da makarantar noma, jihar Bauchi
- Kusa da bankin Wema, Akpakpava Lane, birnin Benin, jihar Edo
- Shataletalen Maiduguri, jihar Borno
- Kusa da filin ƙwallo na jihar Yobe da ke Damaturu, jihar Yobe
- Shataletalen Rainbow da filin ƙwallo na Pantani, jihar Rivers
Jerin wuraren ba cikakke ba ne kuma ana sa ran za a ci gaba faɗaɗa shi.
Ana dai sa ran za a gudanar da zanga-zangar lumanar ne daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024 kan halin ƙunci da yunwar da ake fama da ita a ƙasar nan.
Ƴan sanda sun cafke matashi kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani matashi mai suna Wali Haruna, mazaunin Suleja a jihar Neja, ya shiga hannun ƴan sanda kan kiran matasa su fito zanga-zanga.
Wali Haruna ya yi wani rubutu ne a Facebook yana kiran a shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng