A Hakura da Zanga Zanga: Gwamnati Za Ta Fara Biyan Matasa Alawus na N50000 Duk Wata

A Hakura da Zanga Zanga: Gwamnati Za Ta Fara Biyan Matasa Alawus na N50000 Duk Wata

  • Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin ba da horo ga matasa a yankin Neja Delta karkashin hukumar NDDC
  • Hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) za ta ba matasan horo kan sana'o'in dogaro da kai da nufin inganta rayuwarsu
  • Godswill Akpabio ya ce an ware matasa 10,000 domin a fara da su kuma za su rika karbar alawus na N50,000 duk wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ce matasa 10,000 da hukumar raya yankin Niger Delta za ta horar da su karkashin shirin NIS za su rabauta da N50,000 duk wata.

Sanata Akpabio ya bayyana hakan ne a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers a ranar Talata yayin taro da masu ruwa da tsaki daga NDDC da 'yan yankin Niger Delta.

Kara karanta wannan

NYIF: Matasan da suka nemi tallafin N110bn sun kai 80000, an samu bayanai bayan awanni

Sanata Godswill Akpabio ya yi magana kan tallafawa matasan Niger Delta
Gwamnatin tarayya ta ware N50m domin tallafawa matasa 10,000 duk wata. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Matasa 100,000 za su rabauta da N50,000

Shugaban majalisar dattawan ya ce Shugaba Bola Tinubu ya dukufa ainun wajen ganin yankin Niger Delta ya samu ci gaba, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Akpabio ya ce matasan da za su ci gajiyar wannan tallafin za su kasance sun samu horo kan sana'o'i daban daban da za su bunkasa rayuwarsu.

“Matasa 10,000 za su samu horo a cikin shirin da aka tsara domin inganta sana’o’insu, tare da cewa wadanda suka ci gajiyar shirin a matakin farko za su rika karbar N50,000 duk wata.”

Akpabio ya zayyana muhimman ayyukan NDDC

Jaridar The Punch ta ruwaito shugaban majalisar dattawan, ya roki matasan da su kauracewa zanga-zangar da ake shirin fara yi daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

Ya kara da cewa bayan umarnin shugaban kasa, hukumar NDDC ta kaddamar da wasu manyan ayyuka guda biyar da suka hada da tituna, gadoji, da wutar lantarki a fadin yankin.

Kara karanta wannan

NSDC ta bankado shirin 'yan ta'adda a lokacin zanga-zanga, ta fadi matakin da ta dauka

Sanata Akpabio ya ba da tabbacin cewa aikin titin Legas zuwa Calabar ba wai daga Legas kadai za a fara shi ba, an tsara dauko aikin ne daga Legas da kuma yankin Niger Delta.

Su wanene ke da hannu a zanga zanga?

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya fallasa wadanda ke daukar nauyin matasa su yi zanga-zangar adawa da gwamnati.

Sanata Godswill Akpabio ya ce wadanda suka fadi zaben 2023 ne suka shirya zanga zangar domin hawa mulki ta bayan gida, lamarin da ya ce zai haifar da matsala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.