Arewa: Gwamnonin Sun Dauki Matakin Yaki da 'Yan Bindiga a Jihohi

Arewa: Gwamnonin Sun Dauki Matakin Yaki da 'Yan Bindiga a Jihohi

  • Gwamnonin jihohin Arewa ta yamma sun dauki sabon matakin yaki da yan bindiga da suka fitini al'ummar yankin
  • A yau Talata, 30 ga watan Yuli aka yi taro a Kaduna domin duba yadda za a samu zaman lafiya a yankin Arewa ta yamma
  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayar da shawarwari kan yadda ya kamata a fuskanci matsalolin tsaro a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gwamnonin Arewa ta yamma sun kara daukan matakin yaki da yan bindiga bayan taron samar da tsaro da suka yi a Sokoto.

A wannan karon, an yi taro na musamman da ya hada da kwamishinonin tsaro daga dukkan jihohin Arewa ta yamma.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama boka da ake zargi yana tsafi da kashin ɗan Adam

Uba Sani
An yi taron zaman lafiya domin yaki da yan bindiga a Kaduna. Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda taron ya gudana ne a cikin wani sako da Uba Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin taron zaman lafiya a Kaduna

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa an yi taron ne domin samar da haɗaka wajen yin aiki tare tsakanin jihohin Arewa ta yamma.

Uba Sani ya nuna cewa akwai bukatar hadin kai domin samun damar warware babban abin da ya kawo rashin tsaro a yankin.

Samar da sababbin jami'an tsaro

A yayin taron, gwamna Kaduna ya ba da shawarar samar da jami'an tsaro na musamman da za su rika lura da iyakokin Najeriya da ke hade da Arewa ta yamma.

Gwamnan ya ce hakan zai taimaka matuka ga kwamishinonin tsaro na jihohi wajen toshe ayyukan ta'addanci.

Karin hanyoyin samar da tsaro a Arewa

Kara karanta wannan

Gwamna ya zargi wasu manyan mutane da ɗaukar nauyin zanga zangar da ake shirin yi

Har ila yau, gwamna Uba Sani ya ce dole a bi hanyoyin samar da ilimi da haɓaka noma domin inganta tsaro.

Ya kuma tabbatar da cewa yana da matuƙar muhimmaci a rika damawa da dukkan yan kasa cikin harkokin gwamnati domin samun goyon bayansu.

Zanga zanga: Uba Sani ya yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi taron gaggawa da sarakuna, malamai da jami'an tsaro domin dakile zanga zanga a Kaduna.

Gwamna Uba Sani ya fadi abin da ke kawo musu fargaba da yasa suke ƙoƙarin ganin ba a yi zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng