Ana Shirin Fita Zanga Zanga, Matasa Sun Farmaki Mota Makare da Kayan Abinci
- An yi babban asara bayan wasu miyagu sun farmaki babbar motar bas makare da kayan abinci a jihar Cross River
- Miyagun sun fakaici motar da ke kan hanyarta ta zuwa sakatariyar ƴan jaridu a jihar inda suka tafka musu barna
- Hakan na zuwa ne yayin da ake cikin wani irin hali na tsadar rayuwa da kuma shirin fita zanga-zanga a fadin kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Cross River - Miyagu akalla 100 ne suka farmaki motar bas dauke da kayan tallafi a jihar Cross River.
Bas din makare take da kayan abinci na kungiyar ƴan jaridu a jihar da ta nufi sakatariyar kungiyar.
Matasa sun kai hari kan motar abinci
Vanguard ta tattaro cewa matasan sun yi nasarar kwashe wasu daga cikin kayayyakin abinci bayan fasa tagogin motar a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan yada labarai na hukumar agajin gaggawa ta NEMA a jihar, James Anam shi ya tabbatar da haka ga manema labarai.
Direban motar mai suna Joseph Akpaenin da kyar ya sha da rayuwarsa inda ya ce an dauke masa wayar salula yayin farmakin, Daily Post ta tattaro.
Barnar da aka tafka yayin farmakin
Akpaenin ya ce miyagun sun cigaba da kwashe kayan abincin da ke zuba daga motar inda a lokacin ne ya samu ya tsira da rayuwarsa.
Da yawa daga cikin wadanda suke tawagar sun samu raunuka cikin har da dan jarida daga Tribune inda suke kwance a gadon asibiti.
Hakan bai rasa nasaba da halin kunci da ake ciki na tsadar rayuwa da matsanancin talauci.
"Na biya bukatun masu zanga-zanga" - Tinubu
Kun ji cewa Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ya biya mafi yawan bukatun matasa masu shirin zanga-zanga.
Tinubu ya ce ya dauki wasu matakai masu muhimmanci wadanda za su kawo dauki ga al'umma baki daya duba da halin da ake ciki.
Wannan na zuwa ne yayin da matasa ke shirin fita zanga-zanga a kasar musamman saboda halin kunci da kuma tsadar rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng