Kasa da Kwana 2 a Fara Zanga Zanga, Hukumar Kashe Gobara ta Aika Sako ga 'Yan Najeriya

Kasa da Kwana 2 a Fara Zanga Zanga, Hukumar Kashe Gobara ta Aika Sako ga 'Yan Najeriya

  • A yayin da ake shirin fara zanga-zangar yunwa a fadin kasar, hukumar kashe gobara ta dauki matakan kai daukin gaggawa
  • Hukumar ta ce za ta jibge jami'ai da motoci game da kayan aiki a muhimman wurare yayin da ta yi shirin da ba a taba yi ba
  • Domin kai daukin gaggawa, hukumar ta ba da lambobin waya da 'yan kasar za su iya tuntubar ta domin kashe gobara da hanzari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kashe gobara ta tarayya ta sanar da yin babban shiri da ba a taba yin irinsa ba na karfafa matakan kare kai daga annobar gobara a fadin kasar.

Hukumar karkashin jagorancin Injiniya Jaji O. Abdulganiyu ta dauki wadannan matakan ne domin jiran ko ta kwana yayin da ake gudanar da zanga-zanga.

Kara karanta wannan

'Yan siyasa da kungiyoyi da ke goyon bayan zanga zanga da wadanda suka kushe tsarin

Hukumar kashe gobara ta yi magana kan shirin zanga-zangar yunwa
Ita ma hukumar kashe gobara ta dauki matakai yayin da ake shirin zanga-zanga. Hoto: @Fedfireng
Asali: Twitter

Gangami: Hukumar kashe gobara ta shirya

Sashin yada labarai na hukumar ne ya fitar da sanarwar matakan da aka dauka a shafin FFS na X, inda ya ce matakan sun hada da girke manyan motocin kashe gobara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin matakan da hukumar ta dauka akwai jibge jami'ai da motocin kashe gobara a muhimman wurare da kuma hada kai da jami'an tsaro a fadin kasar.

"An tsara waɗannan matakan ne domin rage haɗarin tsaro kafin, lokacin, da kuma bayan zanga-zangar da aka shirya a duk faɗin ƙasar.
"Shugaban FFS, Abdulganiyu ya bukaci ‘yan kasar da su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da gaggauta kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga hukuma."

- A cewar sanarwar.

Sakon hukumar kashe gobara ga jama'a

Sanarwar ta kuma ce shugaban ya yaba da kwazon ma’aikatan hukumar kashe gobara ta tarayya tare da jaddada jajircewarsu wajen yi wa jama’a hidima.

Kara karanta wannan

Bankwana da tsadar fetur, gwamnati ta dauki mataki 1 na tallafawa matatar man Dangote

Sanarwar ta kara da cewa:

"Hukumar kashe gobara ta tarayya ta sadaukar da kai domin kare rayuka, dukiya, da muhalli daga gobara da sauran iftila'i.
"Da fatan za a kai rahoton duk wani lamari na gobara ko abin da ya shafi bukatar gaggawa ga ofishin kashe gobara na tarayya mafi kusa da ku ko kuma a kira lambobi kamar haka: 112/08032003557."

NSCDC ta tura jami'ai 30,000 zuwa jihohi

A wani labari, mun ruwaito cewa hukumar tsaron farar hula ta dauki nata matakan yayin da ake shirin fara gudanar da zanga-zangar yunwa a fadin kasar.

Hukumar NSCDC ta kuma ce ta gano wani shiri na 'yan ta'adda da suke son mamaye zanga-zangar da ake shirin yi domin lalata kadarorin gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.