'Yan Majalisa 15 Sun Zargi Kyari da Tafka Barna, an Bukaci Shugaban NNPC Ya Yi Murabus

'Yan Majalisa 15 Sun Zargi Kyari da Tafka Barna, an Bukaci Shugaban NNPC Ya Yi Murabus

  • Kungiyar 'ceto tattalin arziki' da wasu 'yan majalisun tarayya suka hada ta nemi shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya yi murabus
  • Shugaban kungiyar kuma dan majalisar wakilai daga Oredo, Hon. Esosa Iyawe ya ce dole Kyari ya yi murabus kan zarge-zargen rashawa
  • 'Yan majalisa si 15 sun yi zargin cewa Kyari da wasu manyan jami'an NNPCL suna tafka barna wanda hakan ya gurgunta gwamnatin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - 'Yan majalisar tarayya 15 karkashin kungiyar 'ceto tattalin arziki' sun bukaci Mele Kyari ya yi murabus daga shugaban kamfanin NNPCL.

Kungiyar 'yan majalisar ta zargi an tafka barna a NNPCL karkashin Mele Kyari, kuma shi ne silar matsalolin da gwamnatin Bola Tinubu ke samu.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga taron FEC a Aso Villa kwanaki 3 gabanin fara zanga zanga

NNPCL: 'Yan majalisar tarayya 15 sun bukaci Mele Kyari ya yi murabus
'Yan majalisar tarayya na so shugaban NNPCL ya yi murabus. Hoto: @nnpclimited, @HouseNGR
Asali: Twitter

'Yan majalisar sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Hon. Esosa Iyawe, dan majlisar wakilai daga Oredo ya fitar a Abuja, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPCL: An nemi Kyari ya yi murabus

Sun dage kan cewa dole ne Kyari ya sauka zuwa lokacin da majalisar wakilai za ta kammala bincike kan halin da kamfanin NNPCL da masana'antar man kasar ke ciki.

'Yan majalisar sun zargi shugaban NNPCL da wasu manyan jami'an kamfanin da nuna yatsa ga shirin gwamnatin Tinubu na 'Renewed Hope.'

Jaridar The Guardian ta ruwaito sun ce Kyari da manyan jami'an NNPCL suna aikata rashawa, kuma suna bata sunan ofishinsu, don haka dole a kore su har zuwa lokacin kammala bincike.

'Yan majalisa sun aika sako ga Tinubu

An ce kwamitin majalisar wakilai na kula da masana'antun mai na kasar yana gudanar da bincike kan zargin akwai masu zagon kasa ga masana'antun man kasar.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri: Ministan Tinubu ya ba 'yan Arewa shawari kan zanga-zangar da ake shirin yi

'Yan majalisar sun nemi Shugaba Bola Tinubu da ya amince Kyari ya yi murabus domin binciken da ake kan zargin NNPCL na ba da lasisin shigo da mai ba bisa ka'ida ba.

Kuma 'yan majalisar sun ce akwai kwamitin da ke bincike kan yadda ake shigo da gurbataccen mai a kasar da kuma amfani da wasu wajen cinikin mai.

Malta: Kyari ya yi wa Dangote martani

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya mayar da martani ga Alhaji Aliko Dangote kan zargin wasu da mallakar gidan mai a Malta.

Kyari ya ce ba shi da wani kamfanin mai a kasar Malta kamar yadda Dangote ya yi zargi inda ya ce kalaman attajirin babu gaskiya a cikin su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.