Daya daga cikin manyan jami'an NNPC ya yi murabus

Daya daga cikin manyan jami'an NNPC ya yi murabus

Shugaban bangaren ayyuka na cigaban kasuwanci a hukumar man fetur ta Najeriya, NNPC, Roland Ewubare ya yi murbus daga hukumar.

The Punch ta ruwaito cewa a ranar Juma'a ne aka gano cewa Ewubare ya yi murabus cikin gaggawa a safiyar ranar Laraba bayan kwashe kimanin shekara biyar yana aiki da hukumar.

Ewubare wanda dan asalin yankin Kudu maso Kudu ne ya yi aiki a matsayin mashawarci na kusa ga marigayi Maikanti Baru, tsohon shugabar hukumar ta NNPC.

Daya daga cikin manyan jami'an NNPC ya yi murabus
Daya daga cikin manyan jami'an NNPC ya yi murabus
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamnan Bauchi ya dakatar da Sarkin Misau

A sakon da ya aike wa majiyar Legit.ng a ranar Juma'a, tsohon shugaban a NNPC ya musanta jita jitar cewa ya yi murabus ne saboda rikicin da suke yi da kamfanin.

Ya ce, "Dan uwa na, babu wata fada. Shugaban hukumar (Mele Kyari) aboki na ne na kut da kut. Ya taimaka min sosai. Na yi murabus ne domin komawa Amurka wurin iyali na.

"Na shafe kimanin shekara biyar a NNPC yawancin lokacin bana tare da su. Saboda annoba, ba zan iya ziyartarsu ba kuma suma ba za su iya kawo min ziyara ba.

"Abinda da wahala. Ni ainihi na mutum ne mai son iyalinsa. Na yi murabus ne saboda in samu lokacin iyali na. Wannan shine gaskiyan batun."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164