Abba Ya Tura Sunan Manjo Janar Majalisa Domin Tantance Shi a Matsayin Kwamishinan Kano

Abba Ya Tura Sunan Manjo Janar Majalisa Domin Tantance Shi a Matsayin Kwamishinan Kano

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake shirya karin kwamishina a jihar inda ya tura sunan Manjo-Janar Muhammad Inuwa
  • Mai girma Gwamna ya tura sunan tsohon sojan domin tantance shi a matsayin sabon kwamishina a jihar saboda inganta shugabanci
  • Wannan na na zuwa ne bayan gwamnan Kano ya kirkiri sababbin ma'aikatu har guda hudu a jihar a watan Maris na shekarar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya tura sunan Manjo-janar Muhammad Inuwa mai ritaya zuwa Majalisar jihar.

Gwamnan ya tura sunan Inuwa ne domin tantance shi a matsayin sabon kwamishina a jihar.

Abba Kabir zai sake nada sabon kwamishina a Kano
Gwamna Abba Kabir ya tura sunan karin kwamishina Majalisar jihar domin tantancewa. Hoto: Abba kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Kano: Abba ya tura karin kwamishina Majalisa

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga taron FEC a Aso Villa kwanaki 3 gabanin fara zanga zanga

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan, Abdullahi I Ibrahim ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo-janar Inuwa mai ritaya ya taba zama kwamandan makarantar sojoji ta NDA da ke jihar Kaduna lokacin yana aiki.

Kafin zama kwamandan NDA, Inuwa ya rike magatakardan Jami'ar Baze da ke birnin Tarayya Abuja bayan ya yi ritaya.

Kano: Abba Kabir ya kirkiri sababbin ma'aikatu

Sannan daga bisani bayanai sun tabbatar da ya rike mukamin shugaban ma'aikata ta jami'an leken asiri na rundunar sojoji.

Manjo-janar Inuwa mai ritaya ya samu damar yin digirin digirgir a Jami'ar tsaro ta Washington DC da ke kasar Amurka.

Abba ya kirkiro sababbin ma'aikatu a Kano

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya kirkiri sababbin ma'aikatu a jihar Kano domin kara inganta shugabanci.

Kara karanta wannan

Gwamna APC a Arewa ya tona asirin masu daukar nauyin ta'addanci a jiharsa

Daga cikin ma'aikatun akwai na tsaron cikin gida da makamashi da jin kai da kuma harkokin ma'adinan kasa.

Burodi: Gwamnati Kano ta shirya daukar mataki

Kun ji cewa hukumar karbar korafe-korafe ta Kano (PCACC) ta gayyaci dilolin fulawa da ke kasuwar Singa da masu gidajen burodi a kan farashin burodi.

Shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya mikawa masu ruwa da tsaki a bangaren samar da burodi gayyatar biyo bayan korafe-korafe da jama'ar gari.

Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce za su zurfafa bincike domin gano musabbabin tsadar burodi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.