“Tinubu Yana Taya Ku Zanga Zangar”: Gwamnati Ta Lissafo Shirin Shugaban ga Matasa
- Yayin da ake shirin fita zanga-zanga a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta bukaci matasa da su dawo daga rakiyar lamarin
- Gwamnatin ta ce mafi yawan bukatun masu zanga-zangar an biya musu wurin kawo tsare-tsaren shawo kan matsalolin
- Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana haka inda ya ce Bola Tinubu ya ji koke-koken jama'a a kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sake yin magana kan zanga-zanga inda ta bukaci matasa su kara ba ta lokaci domin kawo sauyi.
Gwamnatin Najeriya ta ce Shugaba Bola Tinubu yana taya matasan yin zanga-zanga wurin kawo sababbin tsare-tsare masu kyau.
Zanga-zanga: Tinubu ya kawo tsare-tsare masu kyau
Ministan yada labarai, Mohammed Idris shi ya bayyana haka a Abuja a jiya Litinin 29 ga watan Yulin 2024 a cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idris ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta kaddamar da tsare-tsare daban-daban domin ragewa jama'a radadin halin kunci da suke ciki a yanzu.
Ya ce mafi yawan bukatun masu son yin zanga-zangar an dakile su wurin kawo tsare-tsare masu kyau da za su inganta rayuwa, The Guardian ta tattaro.
Gwamnatin Tinubu ta roki masu shirin zanga-zanga
"Mun tabbatar da cewa mafi yawan bukatun masu zanga-zangar an biya musu saboda tsare-tsaren da aka kawo."
"Saboda gwamnatin tana ganin kaman babu bukatar yin zanga-zanga saboda biyan bukatun masu zanga-zangar a Najeriya."
"Kamar yadda muke fada wannan gwamanti ce mai sauraron al'umma, Tinubu ya ji korafe-korafensu domin haka babu bukatar zanga-zanga."
- Mohammed Idris
Shehin malamin Musulunci ya shawarci Tinubu
Kun ji cewa Malamin Musulunci a Gombe, Sheikh Muhammad Adamu Dokoro ya yi magana bayan ziyarar malamai ga Bola Tinubu.
Malamin ya ce babu bukatar su zo ba da hakuri ko kuma tsare-tsaren shugaban wadanda an riga an san su kuma sun wahalar da mutane.
Malamin ya lissafo abubuwa guda biyar wadanda ya kamata shugaban ya dauki matakin gaggawa kansu ba kawai ba mutane hakuri ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng