NSDC Ta Bankado Shirin ’Yan Ta’adda a Lokacin Zanga Zanga, Ta Fadi Matakin da Ta Dauka
- Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta ce ta gano wani shiri na 'yan ta'adda da suke son mamaye zanga-zangar da ake shirin yi
- Babban kwamandan NSCDC, Abubakar Ahmed Audi ya ce manufar 'yan ta'addan ita ce lalata kadarorin gwamnati yayin zanga-zangar
- Yayin da CG Audi ya yarda da 'yancin ’yan Najeriya na yin zanga-zanga, ya gargadin masu shirin shiga rigar matasan su ta da husuma
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babban kwamandan hukumar tsaron farar hula (NSCDC), Dakta Abubakar Ahmed Audi ya ce za a tura jami'an hukumar 30,000 zuwa sassan Najeriya.
CG Abubakar Audi ya ce za a tura jami'an ne domin ba da kariya ga kadarorin kasa a yayin da ake gudanar da zanga-zangar adawa da yunwa a fadin kasar.
Shugaban NSCDC ya bayyana hakan yayin ganawa da kwamandojin shiyya-shiyya na hukumar a hedikwatar NSCDC da ke Abuja, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NSCDC ta bankado shirin 'yan ta'adda
CG Abubakar Audi ya bayyana cewa tura jami'an ya zama wajibi biyo bayan bayanin sirri na suka samu na cewa 'yan ta'adda za su shiga inuwar masu zanga-zangar.
A cewar shugaban na NSCDC, manufar 'yan ta'addar ita ce farwa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba tare da lalata manyan kadarorin gwamnati.
'Yan Najeriya, musamman matasa sun yi ta kiraye-kiraye ga juna da su fita zanga-zanga daga ranar 1 ga watan Agusta domin adawa da tsadar rayuwa.
Tsadar rayuwa a gwamnatin Tinubu
Tsadar rayuwa ta ta'azzara a Najeriya bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen tallafin man fetur tare da sassauta tsarin musayar kudaden waje bayan hawansa mulki.
Hauhawar farashin kayayyaki ta kai kashi 34.19 a cikin watan Yuni, tare da hauhawar farashin abinci zuwa sama da kashi 40.87, a cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasa.
Yayin da take amincewa da 'yancin ’yan Najeriya na yin zanga-zanga, NSCDC ta ce dole ne a yi ta cikin lumana, tana mai gargadin masu shirin lalata kadarorin gwamnati.
Kwanaki biyu da suka gabata, a sanarwar da ta fitar a shafinta na X, NSCDC ta ce ta tsaurara matakan tsaro a inda kadarorin gwamnati suke.
Zanga-zanga: 'Yan sanda sun dauki mataki
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sanda a birnin Tarayya Abuja ta tura jami'anta akalla 4,200 domin dakile miyagu da za su shiga cikin masu zanga-zangar.
Mai magana da yawun rundunar, Josephine Adeh ta bayyana haka a ranar Juma'a 26 ga watan Yulin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng