FG za ta kafa hukumar kula da kadarorin gwamnati da aka kwato

FG za ta kafa hukumar kula da kadarorin gwamnati da aka kwato

> Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na kafa wata hukuma da za ta kula da kadarorin da aka kwato daga hannun mabarnata tattalin arzikin kasa

> Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya sanar da manema labarai cewa kafa sabuwar hukumar zai karawa yaki da cin hanci armashi da ma'ana

- Ya bayyana cewa a baya hukumomi da dama ne suke gudanar da aikin kwace da kulawa da kadarorin da aka karbe daga hannun mabarnata

Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da kafa wata hukuma da za ta kula da kadarorin da aka kwato daga hannun mabarnata da ma su yi wa tattalin arziki zagon kasa.

Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ne ya sanar da hakan ga manema labarai.

Ya sanar da hakan ne yayin ganawarsa da 'yan jarida a fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron FEC na wannan makon.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne ya jagoranci taron wanda aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo a fadar shugaban kasa.

A cewar Malami, kudirin neman kafa hukumar ya gama fayyace irin yanayi da hurumin aiyukanta.

Babban aikin hukumar shine samar da tsarin tattarawa tare da kula da kadarorin gwamnati da aka kwato.

A cewar ministan, hakan zai kawo karshen sabanin da hukumomi ke samu a kan kula da kadarorin da gwamnati ta kwato.

Ya bayyana cewa da zarar kudirin ya zama doka kuma an kafa hukumar, babu sauran wani rudani dangane da kadarorin gwamnati da aka kwato.

"Akwai bukatar samar da wasu dokoki dangane da kadarorin gwamnati da aka kwato.

"Ana kwato irin wadannan dukiyoyi ne daga hannun ma su laifi, akwai bukatar samar da tsari da dokoki a kan yadda za a adanasu da kuma sarrafasu.

"A baya kadarorin da aka kwato su na hannun hukumomi daban-daban kamarsu DSS, EFCC, da ICP da sauransu.

"Kafa wannan sabuwar hukumar zai karawa yaki da cin hanci armashi da ma'ana," a cewar Malami.

FG za ta kafa hukumar kula da kadarorin gwamnati da aka kwato
Abubakar Malami
Asali: Twitter

A ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa an dan samu yamutsi bayan shugaban kwamitin bincike, Ayo Salami, ya umarci wasu lauyoyin Magu su fice daga dakin da da kwamitin ke zamansa a fadar shugaban kasa.

Ayo Salami ne shugaban kwamitin bincike da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa domin bankado cin hanci da kwato kadarorin gwamnati.

KARANTA: Kano: Mutane uku sun mutu sakamakon rushewar wani a gini a Dawanau

KARANTA: Yakin neman zabe: Atiku ya mayar wa Tinubu martani a kan zaben Edo

Salami ya umarci jami'an tsaro su fita da wasu lauyoyin Magu guda biyu; Zainab Abiola da Aliyu Lemu, jim kadan bayan gabatar dasu.

An fara samun matsala ne bayan Wahab Shitu, shugaban tawagar lauyoyin Magu, ya mike domin gabatar da sauran abokan aikinsa.

Sai dai, Salami ya katsewa Shittu hanzari ta hanyar sanar da shi cewa shine kadai za a bari ya kare Magu.

Bayan hakan ne sai ya umarci jami'an tsaro su fitar da sauran lauyoyin.

An fara binciken Magu ne bisa zarginsa da almundahana da kuma rashin biyayya, kamar yadda ministan shari'a, Abubakar Malami, ya rubuta korafi a kansa zuwa fadar shugaban kasa.

Har yanzu kwamitin Salami ya na cigaba da gudanar da bincike a kan Magu duk da an bayar da shi beli.

Shugaba Buhari ya kafa kwamitin ne domin gudanar da bincike tare da kwato kadarorin gwamnati daga hannun wasu manyan jami'an gwamnati; na baya da na yanzu, da ake zargi da almundahana, waskiya, ko sama da fadin kudi, dukiya ko wata kadara mallakar gwamnati.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng