Matasa Sun Zama Kishiyoyin 'Yan Zanga Zanga, Sun Yi Tattakin Goyon Bayan Tinubu
- Wasu matasa a jihar Legas sun yi tattakin nusar da sauran yan kasar nan illar gudanar da zanga-zanga adawa da manufofin APC
- A ranar 1-10 Agusta, 2024 ne wasu 'yan Najeriya su ka shirya fita tituna domin nuna bakin cikinsu kan matsin rayuwa a kasar nan
- Matasan Legas sun nuna goyon bayansu ga manufofin gwamnatin tarayya, inda su ke neman sauran matasa su yi watsi da zanga-zanga
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Legas - Matasa a jihar Legas sun yi tattaki domin nusar da sauran jama'ar kasar nan illar gudanar da zanga-zanga a makon nan.
A ranar 1 Agusta ne wasu 'yan kasar nan su ka shirya fita zanga-zangar gama gari, a yunkurinsu na shaidawa gwamnati halin da su ke ciki.
A sakon da wani mai amfani da shafin X, Ayo, the First ya wallafa, an ga bidiyo da hotunan matasa dauke da sakonnin da ke neman a yi watsi da zanga-zanga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nemi matasa su watsar da zanga-zanga
Jaridar The Nation ta tattaro yadda wasu matasa su ka shawarci takwarorinsu a fadin kasar nan da su yi watsi da batun fita zanga-zanga.
Matasan da su ka hallara daga sassa daban-daban na jihar sun hadu a Legas Island tare da rokon sauran jama'ar da kar su biyewa zanga-zangar tashe -tashen hankula.
Matasa sun tuna illar zanga-zangar EndSARS
Matasan sun bayyana cewa bai kamata a maimaita asarar rayuka da dukiyoyi kamar yadda aka yi a zanga-zangar EndSARS ba.
Matasan sun nuna rashin jin dadin yadda aka tafka asara a wancan lokaci, tare da neman hadin kai kar a maimaita irin waccan asarar.
Zanga-zanga: An samu baraka tsakanin kungiyar Yarbawa
A wani labarin kun ji yadda kungiyar yarbawa ta rabu gida biyu a kan batun zanga-zangar adawa da manufofin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyar da ke tsagin Ayo Adebanjo ta ce kowa ya fito a yi zanga-zanga, yayin da daya tsakin karkashin jagorancin Reuben Fasoranti ya barranta kansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng