'Yan Najeriya Sun Mamaye Ofishin MTN, an Gano Dalilin Rufe Layukan Jama’a

'Yan Najeriya Sun Mamaye Ofishin MTN, an Gano Dalilin Rufe Layukan Jama’a

  • Daruruwan masu amfani da layin MTN ne suka mamaye babban ofishin kamfanin da ke Ibadan, jihar Oyo a safiyar Litinin
  • An ruwaito cewa kamfanin sadarwa na MTN ya rufe layukan mutane da dama a ranar Lahadi bisa zargin sun ki hada su da NIN
  • Sai dai wasu daga cikin wadanda abin ya shafa da suka zanta da Legit Hausa sun bayyana cewa sun hada layukansu da NIN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Daruruwan masu amfani da layin MTN ne da cibiyar sadarwar ta rufe masu layukansu sun yi wa ofishin kamfanin da ke Ibadan, jihar Oyo kawanya a safiyar ranar Litinin.

Kamfanin MTN mafi girma a Najeriya da ke da miliyoyin masu amfani da shi ya rufe layukan mutane da dama a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

NNPC ya aika sako ga ƴan Najeriya yayin da gidajen mai suka fadi sabon farashin fetur

Jama'a sun mamaye ofishin MTN a jihar Oyo
'Yan Najeriya da aka rufewa layukan waya sun mamaye ofishin MTN a Oyo.
Asali: Getty Images

MTN ya yi ikirarin cewa wadanda aka rufe masu layukansu sun gaza hada lambar NIN dinsu da layukan nasu kamar yadda kamfanin ya umurta, inji rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MTN ya rufe layukan jama'a

An ce wasu daga cikin jama’ar da aka rufewa layinsu sun tayar da tarzoma a ofishin inda har suka rika jefa duwatsu a cikin ginin kamfanin.

Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa, sun yi zargin cewa kamfanin ya yi hakan ne a wani bangare na kokarin dakile zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka shirya gudanarwa a fadin kasar a ranar Alhamis.

Bayanai sun nuna idan aka samu sabanin bayanai wajen rajista da NIN, ana rufe layi.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa har ya zuwa lokacin wannan rahoto, kamfanin sadarwa bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan takaddamar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da suka jawowa gwamnatin Tinubu zanga zanga bayan shekara 1

Hakazalika, Legit Hausa ba ta iya samun tabbacin adadin layukan da MTN ya rufe ba da kuma matakin da masu layukan za su bi domin a bude masu.

Masu amfani da MTN sun yi korafi

A zantawarmu da wata Hauwa'u Lawal Mailafia, ta shaida mana cewa MTN sun rufe mata layinta amma ita ta fi shekara da hada shi da NIN kuma har shaidar hakan sun tura mata.

Malama Hauwa'u ta ce abin da MTN suka yi mata ba ta ji dadinsa ba domin sun ja mata asarar abokan cinikin da take aika masu da awara idan ta kammala sakamakon rufe layinta.

Ita ma Himnas Abubakar, wata malamar koyar da sabulun gargajiya, turarurruka da dai sauransu, ta ce MTN sun rufe layin da ta fi amfani da shi amma basu rufe dayan ba.

Ta ce a rana daya ta yi wa duka layukan nata rijista da NIN, amma abin mamaki sai suka rufe wanda ta fi mu'amala da shi ba su rufe wanda yanar gizo kurum ta ke hawa da shi.

Kara karanta wannan

Kwara: Miyagun 'yan bindiga sun farmaki masu ibada, 'yan sanda sun kai daukin gaggawa

NCC ta umarci a rufe layukan jama'a

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NCC ta ba kamfanonin sadarwa izinin toshe layukan waya da ke aiki ba tare da an hada su da lambobin NIN ba.

Kamfanonin MTN, Airtel, Glo, 9mobile, da sauransu za su fara aiwatar da umurnin daga yau, Laraba, 28 ga watan Fabrairun 2024 kamar yadda sanarwar NCC ta nuna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.