Kamfanin MTN ta biya Najeriya Biliyan 165 cikin Biliyan 330 da ake bin ta
- Najeriya na bin kamfanin nan na MTN kudi har Naira Biliyan 350
- An makawa MTN taran kudi ne bayan sun sabawa wata yarejeniya
- Yanzu MTN dai na cigaba da biyan wannan kudi sannu a hankali
Mu na da labari cewa Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu makudan Biliyoyin kudi daga hannun Kamfanin sadarwar nan na MTN a dalilin wasu tara da aka ci kamfanin a baya na kun rufe wasu layuka miliyan 5.
Farfesa Umar Garba Danbatta wanda shi ne Shugaban Hukumar sadarwa na Najeriya watau NCC ta tabbatar da cewa kamfanin MTN ta biya Naira Biliyan 165 a matsayin tara na wasu layuka rututu da ba ayi wa rajista ba a kasar.
KU KARANTA: Hannun jari sun yi kasa a Najeriya bayan Buhari yace zai yi takara a 2019
A kwanakin baya dai Gwamnatin Najeriya ta maka makudan taran kudi kan MTN na kasar Afrika ta Kudu na sabawa yarjejeniyar da aka yi da su wanda ke da barazana ga tsaron kasar. Yanzu dai an biya rabin kudin inji NCC.
A jiya ne Umar Garba Danbatta ya bayyanawa manema labarai cewa Kamfanin MTN ta hannun Shugaban ta na Najeriya Dr Pascal Dozie ta kara biyan Najeriya Biliyan 55 a watan jiya na Maris kamar yadda aka yi alkawari.
Ga dai yadda ake biyan Najeriya kudin nan bayan an yi wa kamfanin rangwame. Taran dai ya sa kamfanin MTN ya gaza cin riba a bara.
A karshen Maris na 2017 an biya Najeriya Biliyan 30
A karshen Maris na 2018 an biya Najeriya Biliyan 55
A karshen Disamba na 2018 za a biya Najeriya Biliyan 55
A karshen Maris na 2019 za a biya Najeriya Biliyan 55.
A karshen Mayu na 2019 za a biya Najeriya Biliyan 25
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng