Dubun Dan Majalisa, Hakimai Masu Hada Baki da 'Yan Bindiga Ta Cika a Jihar Arewa

Dubun Dan Majalisa, Hakimai Masu Hada Baki da 'Yan Bindiga Ta Cika a Jihar Arewa

  • Wani ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara ya shiga hannun ƴan sanda bisa zargin haɗa baki da ƴan bindiga
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar ya tabbatar da cewa Aminu Ibrahim mai wakiltar Kauran Namoda yana tsare a hannunsu bisa zargin yin garkuwa da mutane
  • Kwamishinan ya kuma bayyana cewa wasu Hakimai biyu na tsare a hannunsu kan zargin yin aiki tare da ƴan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar Kauran Namoda, Aminu Ibrahim, na daga cikin waɗanda ake zargi da haɗa baki da ƴan bindiga.

Ɗan majalisar yana tsare a hannun ƴan sanda bisa zargin yin garkuwa da mutane.

'Yan sanda sun cafke dan majalisa a Zamfara
'Yan sanda sun cafke dan majalisa kan zargin hada baki da 'yan bindiga a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Muhammad Shehu Dalijan, ya tabbatar da cafke ɗan majalisar yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Matasa na shirin zanga zanga, jami'an tsaro sun harbe ƴan fashi har lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka cafke ɗan majalisar?

Muhammad Dalijan ya ce an kama Aminu Ibrahim ne bisa zarginsa da hannu wajen sace Alhaji Ibrahim Sarkin Fada mai shekaru 80 a ƙauyen Kasuwar Daji.

Ya kuma bayyana cewa Hakimin Kauran Namoda, Alhaji Jafaru Abdullahi Kumburki da tsohon shugaban ƙaramar hukumar, Nasiru Muhammad, suna hannun ƴan sanda bisa irin wannan zargi.

Hakimai na haɗa baki da ƴan bindiga

Kwamishinan ƴan sandan ya ce ana binciken Hakimai uku na Danjibga, Bukkuyum da Unguwar Gyauro a ƙananan hukumomin Tsafe da Bukkuyum, waɗanda ba a bayyana sunayensu ba, kan haɗa baki da ƴan bindiga.

Ya ce binciken farko da ƴan sanda suka gudanar ya nuna cewa Hakimin Kauran Namoda ya haɗa baki da wasu mutane biyu, Alhaji Bala da Hadi Sidi da ake zargin masu taimakawa ƴan bindiga ne.

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin kamfen PDP ya mayar da zazzafan martani ga Atiku kan zanga zanga

Ya bayyana cewa sun haɗa baki tare da yin garkuwa da mutane tara a ƙauyen Gidan Sambo da ke ƙaramar hukumar Kauran Namoda.

Kwamishinan ƴan sandan ya ce mutanen uku sun karɓi kudin fansa N800,000 kafin su sako mutanen da suka yi garkuwa da su.

Manyan mutane na garkuwa da mutane

Kwamishinan ya ce tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kauran Namoda, wanda yake a tsare, ana zarginsa da haɗa baki da Hali Sidi da Alhaji Bala wajen yin garkuwa da wani Alhaji Ango na ƙauyen Kumurya.

"Har yanzu ana ci gaba da bincike kuma ina tabbatar muku cewa duk wanda aka samu da hannu za a gayyace shi domin amsa tambayoyi."

- Muhammad Dalijan

EFCC za ta binciki ɗan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta sha alwashin cafke ɗan majalisar tarayya bisa zargin ɗaukar nauyin ta'addanci.

Kara karanta wannan

Tinubu na shirin rattaba hannu kan kudirin dokar mafi karancin albashi

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabun Kaura Namoda da Birnin Magaji, Aminu Sani-Jaji ne hukumar ke zargi da taimakawa ƴan ta'adda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng