Sauki ya Kusa Samuwa: Farashin Kayan Abinci ya Fara Sauka a Kasuwar Kano

Sauki ya Kusa Samuwa: Farashin Kayan Abinci ya Fara Sauka a Kasuwar Kano

  • Yayin da ya rage kwanaki biyu 'yan Najeriya su shiga zanga-zanga saboda yunwa da tsadar kayan abinci, farashin abinci ya fara sauka a Kano
  • A wata hira da ta kebanta da Legit, shugaban kasuwar abinci ta Dawanau a Kano, Mustapha Maikalwa ya ce farashin masara da gero ya fara sauka
  • A cewarsa daga nan zuwa makonni hudu, sabon abinci zai shiga kasuwanni kuma dole farashi ya sauka tun da abincin zai samu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Farashin kayan abinci da ke daya daga matsalolin da Najeriya ke fuskanta ya fara saukowa saboda shigowar sabon abinci kasuwa.

Kara karanta wannan

Sauki zai zo nan kusa: Siminti zai sauka, BUA ya gano hanyar sauke farashi kayansa a Najeriya

Damuna ta fara albarka yayin da farashin hatsi ya fara alamun sauka a kasuwar hatsi ta Dawanau da ke Kano wanda tana cikin manya a nahiyar.

Abinci
Farashin hatsi ya fara sauka a kasuwar hatsi Hoto: Mohammed Owais Khan
Asali: Getty Images

A zantawarsa da Legit, shugaban kasuwar Dawanau, Mustapha Maikalwa ya ce ana sayar da buhun gero a kan 87,000, ita kuma masara 85,000, amma ya fara sauka yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Farashin abinci zai sauka sosai," Maikalwa

Shugaban kasuwar Dawanau Mustapha Maikalwa ya bayyana cewa yanzu haka ana sayar da buhun gero a kan N78,000, N80,000, N81,000 ko N82,000.

AlhajiMustapha Maikalwa ya ce abin ya danganta da inda mutum ya je sayayya a kasuwar.

Ya kara da cewa wannan sauki ne idan aka kwatanta da yadda ake sayar da shi a kan N87,000 a makonnin baya.

Maikwalwa ya ce ita kuma masara da ake sayarwa a kan N85,000 yanzu ana sayar da ita a kan N80,000.

Kara karanta wannan

"Gaskiyar abin da ya jawo ake shirin yin zanga-zanga", Farfesa Kperogi ya fasa ƙwai

"Sayen nauyi; wanda zai sayi kamar kilo ko tirela daya, zai iya samunta a kan N75,000, sayen dai-dai kuma N80,000."

- Shugaban kasuwar Dawanau, Mustapha Maikwalwa

"Farashin abinci zai sauka," Gwamnati

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce ta dauki hanyar shawo kan matsalar hauhawar farashin abinci a fadin kasar nan biyo bayan yadda 'yan kasa ke kokawa.

Ministan noma da albarkatun kasa, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka inda ya ce sun samar da ingantaccen tan 60,432 na iri da zai taimaka wajen habaka noma da rage tsadar abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.