Sauki Zai Zo Nan Kusa: Siminti Zai Sauka, BUA Ya Gano Hanyar Sauke Farashi Kayansa a Najeriya

Sauki Zai Zo Nan Kusa: Siminti Zai Sauka, BUA Ya Gano Hanyar Sauke Farashi Kayansa a Najeriya

  • Abdul Samad Rabiu, shugaban kamfanin BUA Group, ya yi shirin farantawa ‘yan Najeriya rai game da farashin siminti
  • Attajirin ya ambaci farfadowar Naira da kuma kara yawan samar da kayayyakin kamfanin ke yi a matsayin sanadin kawo sauyin farashin
  • BUA dai shi ne kamfani na biyu mafi girma wajen samar da siminti a Najeriya bayan Dangote kuma yana kokarin fadada ayyukansa

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Najeriya - Farashin siminti a Najeriya na iya raguwa nan ba da jimawa ba, a cewar Abdul Samad Rabiu, wanda ya kafa kamfanin BUA Group.

Duk da haka, Abdul ya lura cewa farashin siminti a yanzu a Najeriya ya fi na sauran kasashen nahiyar Afrika sauki nesa ba kusa ba.

Kara karanta wannan

"Da Tinubu bai ci zaben 2023 ba," Minista ya fadi halin da Najeriya za ta shiga

BUA za su rage farashin siminti
Farashin siminti zai sauka nan kusa | Hoto: BUA
Asali: Getty Images

Da yake zantawa a wani taron dabaru da kuma murnar hadakar BUA da kamfanin CBMI na China ya ce, rage farashin na zuwa ne saboda karuwar darajar Naira da aka samu kwanan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufar BUA na samar da kayayyaki ga ‘yan kasa

Ya kuma bayyana cewa, BUA na aiki tukuru wajen tabbatar da habaka hanyar samar da siminti a wata ma’aikata da yake ginawa a jihar Edo.

A cewarsa, ana aikin ne don tabbatar da wadatuwar siminti da sauran kayayyaki ga ‘yan gida Najeriya da ma fitarwa kasashen waje.

Jaridar The Nation ya ruwaito cewa, shugaban BUA ya ce kamfanin na nan kan manufarsa na ci gaba da kasancewa akalla na biyu wajen samar da siminti a kasar.

Yaushe za a fara aikin kamfanin BUA?

A cewarsa:

“Wannan zubi na hudu na kamfanin zai samar da kadada miliyan uku a shekara, kuma za a fara aikinsa nan kusa, watakila Asabar ko Lahadi.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da suka jawowa gwamnatin Tinubu zanga zanga bayan shekara 1

“Tuni an ba da sabon kwangilar ginin kuma an cike duk wasu takardu, za a kammala nan da watanni 20. Muna murna da farin cikin hada kai da CBMI.”

Hakazalika, ya yi magana kan yiwuwar samar da hanyoyin fitar da kayayyakinsa waje daga ma’aikatarsa ta Sokoto zuwa Nijar da Burkina Faso.

Yadda farashin siminti ya tashi a 2024

A tun farko, rahotannin da muke samu yanzu haka na nuni da cewa ana siyar da buhun siminti tsakanin naira 10,000 zuwa naira 11,000 a yankin Idimu dake jihar Legas.

Hakan ya faru ne duk da yarjejeniyar da aka cimma da masana’antun sarrafa simintin da gwamnatin tarayya na cewa a sayar da siminti kan naira dubu bakwai.

Wata dillalin siminti mai suna Alhaja, ta shaidawa The Nation cewa ana yaudarar mutane ne kawai da cewa za a sayar da siminti akan naira dubu bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.