Zanga Zanga: Sheikh Bello Yabo Ya Yi Magana, Ya Ragargaji Duka Bangarorin
- Sheikh Bello Yabo ya bayyana matsayarsa kan zanga-zanga inda ya ce shi bai ce a yi ko kada a yi ba inda ya shawarci malamai
- Shehin malamin ya ce idan har zanga-zangar lumana ce ba matsala amma fa su sani wasu na iya shiga lamarin domin bukatarsu
- Bello Yabo ya gargadi malamai da su bar shiga lamarin saboda idan haushin Bola Tinubu ya fara kama su ba za su ji da kyau ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Malamin Musulunci, Sheikh Bello Yabo ya yi magana kan masu zanga-zanga da kuma shawara gare su.
Sheikh Yabo ya ce tun farko bai yi magana kan zanga-zanga ba saboda bai ga abin da zai ce ba amma bai hana ba kuma bai ce a yi ba.
Zanga-zanga: Sheikh Bello Yabo ya yi magana
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da Karatuttukan Malaman Musulunci ta wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehin malamin bukaci jama'a su girmama malaman addini kamar yadda suke girmama malaman boko a kowane lokaci.
"Idan dai zanga-zanga ne shege ka fasa ga fili nan akwai wanda aka ce kada ya fito, su ma malaman da ke cewa kada a yi ku kyale su."
"Waye za ka shiga wa fada talakawan da ba su san ciwon kansu ba ko azzaluman shugabannin zaka shiga wa fada?"
"Su talakawa jiki na ya mutu a kansu, shugabanni kuma daman ba na tare da su, daman mun san inda muka ajiye su."
- Sheikh Bello Yabo
Bello Yabo duk da an ce zanga-zanga ce ta lumana Allah yasa a yi lafiya a kare lafiya, yasa wadanda aka yi dominsu su gyara.
Ya ce farfaganda ta malamai ba zai yiwu ba, mai jin yunwa bai jin wa'azi, idan yana jin yunwa abinci yake bukata ba wa'azi ba.
Har ila yau, ya shawarci shugabannin su yi abin da ya dace inda ya gargadi malamai su yi hankali kada haushin Tinubu ya kama su.
Daurawa ya yi magana kan shugabanni
Kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun sauke nauyin da aka daura musu na fadan gaskiya ga shugabanni.
Daurawa ya ce idan har aka samu matsala to ko daga bangaren shugabannin ne ko kuma matasa ba su ji maganar da aka yi ba.
Asali: Legit.ng