“Talauci Ne Ke Damunku”: Fitaccen Mawaki Ya Soki Masu Shirin Zanga Zanga

“Talauci Ne Ke Damunku”: Fitaccen Mawaki Ya Soki Masu Shirin Zanga Zanga

  • Mawaki Habeeb Okikiola ya dira kan masu zanga-zanga inda ya ce talauci da rashin aiki ne yake yaudarar matasan da ke son fita
  • Mawakin da aka fi sani da Portable ya ce a baya ya fita zanga-zanga amma lokacin ba shi da ko kwabo amma yanzu ya tsira
  • Portable yayi wannan martani ne yayin da matasa a Najeriya suka shirya fita zanga-zanga a ranar 1 ga watan Agustan 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Fitaccen mawaki a Najeriya, Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya yi magana kan masu zanga-zanga.

Portable ya ce ba zai taba fita zanga-zanga ba da ake shirin yi musamman saboda halin kunci da ake fama da shi a kasar.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa zanga-zangar cire tallafi a mulkin Jonathan ba a samu rigima ba'

Mawaki ya caccaki masu son fita zanga-zanga
Fitaccen Mawaki, Portable Ya Soki Masu Shirin Zanga Zanga a Najeriya. Hoto: #portablebaeby.
Asali: Instagram

Zanga-zanga: Portable ya yi magana matasa

Mawakin ya fadi haka a wani faifan bidiyon Instagram inda ya ce a shekarar 2020 an dama da shi a wurin zanga-zanga amma yanzu ya samu cigaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Portable ya bukaci magoya bayansa da su mayar da hankali wurin inganta rayuwarsu madadin shiga lamarin zanga-zanga.

Ya ce kwata-kwata zanga-zanga ba na masu hali ba ne saboda lokacin da ya yi yana matsiyaci ne shi yasa amma yanzu ya tsira.

"Masoyana, wasu sun ce wai na shiga zanga-zanga a 2020, tabbas haka ne amma lokacin ina talaka ne, yanzu kuma ina da kudi."
"Kun taba ganin Femi Otedola ko Aliko Dangote da Dele Momodu suna zanga-zanga a rayuwarku?"
"Lokacin ina tunani kamar talaka wanda ba shi da komai, yanzu kuma ina da kudi, masu kudi ba su yin zanga-zanga."

- Portable

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun sake magana kan zanga-zanga, sun fadi manaƙisar da ke ciki

Portable ya shawarci matasa su nemi kudi

Portable ya ce ba zai taba sassautawa wanda ya bukace shi da ya je wurin zanga-zanga domin yin waka ba inda ya ce su ma su dauki abin magana su yi waka.

Ya ce idan mutum yana da aikin da yake yi babu abin da zai saka shi fita zanga-zanga inda ya ce kowa ya nemawa kansa mafita ba Najeriya ba.

"Najeriya dai-dai take kune ba ku daidaita ba, kudi suna inda suke kune wadanda ba ku aiki shiyasa ba ku same su ba."

- Portable

'Yan sanda sun gidaya sharuda kan zanga-zanga

Kun ji cewa rundunar 'yan sanda a Najeriya ta amince da yin zanga-zanga amma ta lumana tare da gindaya wasu sharuda.

Rundunar ta ce za ta ba da kariya amma matasan za su tura bayanansu ga kwamishinonin jihohinsu domin samar da tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.