Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Bayan Mutuwar Sanatan APC, Ya Yi Addu’a

Tinubu Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Bayan Mutuwar Sanatan APC, Ya Yi Addu’a

  • Shugaba Bola Tinubu ya kadu da samun labarin rasuwar Sanata Ifeanyi Ubah da ke wakiltar Anambra ta Kudu a birnin Landan
  • Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da abokansa da ma al'umma da gwamnatin jihar Anambra kan wannan rashi
  • Hakan ya biyo bayan rasuwar marigayin kamar yadda Majalisar Dattawa ta fitar bayan ya yi fama da jinya na wani lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tura sako ga iyalan Sanata Ifeanyi Ubah bayan sanar da mutuwar dan Majalisar a Landan.

Shugaban ya kuma tura sakon ta'aziyya ga 'yan uwa da abokan marigayin inda ya ce tabbas wannan abin takaici ne.

Kara karanta wannan

Sunayen Sanatoci da ‘Yan majalisar tarayya 6 da mutuwa ta dauke bayan cin zaben 2023

Tinubu ya rude bayan samun labarin rasuwar sanatan APC
Bola Tinubu ya tura sakon ta'aziya ga iyalan Sanata Ifeanyi Ubah. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Senator Dr. Patrick Ifeanyi Ubah.
Asali: Facebook

Tinubu ya jajantawa iyalan sanata Ifeanyi Ubah

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren sadarwa, Ajuri Ngelale ya fitar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi addu'ar samun rahama ga mamacin inda ya ce tabbas an tafka babban rashi wanda maye gurbinsa zai yi wahala.

Shugaban ya kuma jajantawa Majalsiar Dattawa da al'umma da kuma gwamnatin jihar Anambra kan wannan babban rashi.

Ubah: Tinubu ya yi addu'a ga marigayin

"Shugaba Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi Sanata Ifeanyi Ubah."
"Marigayin ya kasance hamshakin dan kasuwa kuma dan siyasa, ya wakilci mazabar Anambra da Kudu a Majalisar Dattawa."
"Shugaba Tinubu ya jajantawa abokansa da Majalisa da gwamnati da kuma al'ummar jihar Anambra bisa wannan babban rashi."
"Shugaban ya yi addu'ar samun rahama ga marigayin tare da ba iyalansa hakurin jure rashinsa."

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Majalisar Dattawa ta sanar da mutuwar fitaccen sanatan APC

- Bola Tinubu

Sanatan APC, Ifeanyi Ubah ya rasu

Mun baku labarin cewa sanatan jam'iyar APC da ke wakiltar Anambra ta Kudu, Ifeanyi Ubah ya riga mu gidan gaskiya.

Sanatan ya rasu ne a yau Asabar 27 ga watan Yulin 2024 a dakin otal da ke birnin Landan a kasar Burtaniya bayan rashin lafiya.

Sanatan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a farkon shekarar 2024 inda ya ke neman takarar kujerar gwamnan jihar Anambra a 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.