An Shiga Jimami Bayan Sanatan APC Mai Ci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Shiga Jimami Bayan Sanatan APC Mai Ci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa Sanata Ifeanyi Ubah ya riga mu gidan gaskiya kwanaki kadan bayan barin Najeriya
  • Marigayin dan jam'iyyar APC da ke wakiltar Anambra ta Kudu ya rasu ne a dakin otal da ke birnin Landan a kasar Burtaniya
  • Ubah kafin rasuwarsa, ya ba da gudunmawar N71m ga APC a jiharsa a kokarin kwace mulkin jam'iyyar APGA daga Charles Soludo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - An shiga jimami bayan rasuwar Sanata Ifeanyi Ubah da ke wakiltar Anambra ta Kudu a Majalisar Dattawa.

Sanatan wanda dan jam'iyyar APC ne a ya rasu ne a dakin otal da ke birnin Landan a Burtaniya kwana biyu bayan barin Najeriya.

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Majalisar Dattawa ta sanar da mutuwar fitaccen sanatan APC

Sanatan Najeriya ya riga mu gidan gaskiya a birnin Landan
Sanatan Anambra ta Kudu, Ifeanyi Ubah ya rasu a andan. Hoto: Ifeanyi Ubah.
Asali: Facebook

Yaushe sanatan APC, Ifeanyi Ubah ya rasu?

Leadership ta tattaro cewa marigayin ya rasu ne da safiyar yau Asabar 27 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai da ba a fayyace ainihin dalilin mutuwar marigayin ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Rashin lafiyar Ubah ta kara yin kamari ne a cikin awanni 48 wanda hakan ya yi sanadin rasa ransa a Landan, cewar The Guardian.

Ifeanyi Ubah: Musabbabin sauya shekarsa zuwa APC

An zabi Ubah a matsayin sanata a jam'iyyar YPP a 2019 inda a sake zarcewa zuwa Majalisar a shekarar 2023.

Ubah ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a farkon wannan shekara ta 2024 inda ya nuna sha'awar tsayawa takara a zaben Anambra a 2025.

An tabbatar cewa kafin rasuwarsa da kwanaki ya ba da gudunmawar N71m ga jam'iyyar APC a Anambra.

Kara karanta wannan

Fargabar zanga zanga: Ganduje ya gana da ciyamomi APC a jihohi, bayanai sun fito

Ya ba da gudunmawar domin kara karfn jam'iyyar a jihar yayin da ta ke kokarin kwace mulki daga hannun Charles Soludo.

APC ta gana da ciyamomi kan zanga-zanga

Kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya kira wata ganawa da shugabannin APC a jihohi 36 a kasar.

Ganawar ba ta rasa nasaba da shirin zanga-zanga a fadin kasar da matasa suka shirya saboda mawuyacin hali da ake ciki.

Sakataren jam'iyyar a kasa, Felix Morka shi ya tabbatar da haka a jiya Juma'a 26 ga watan Yulin 2024 da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.