Uju Ohaneny: Lokuta 6 da Ministar Mata Ta Jawowa Gwamnatin Tinubu Abin Magana

Uju Ohaneny: Lokuta 6 da Ministar Mata Ta Jawowa Gwamnatin Tinubu Abin Magana

FCT, Abuja - A watan Agusta, Bola Ahmed Tinubu ya nada Uju Kennedy-Ohanenye a matsayin Ministan harkokin mata a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Daga lokacin da ta shiga ofis zuwa yanzu, Uju Kennedy-Ohanenye ta yi ta jawo abubuwan magana wadanda Legit ta tattaro wasu a nan.

Rikicin Uju Kennedy-Ohanenye tana Minista

Uju Kennedy-Ohanenye
Ministar Mata, Barrister (Mrs) Uju Kennedy-Ohanenye Hoto: fmino.gov.ng
Asali: UGC

1. Uju Kennedy-Ohanenye da majalisar dinkin duniya

Ba ta dade da shiga ofis ba, Uju Kennedy-Ohanenye ta yi wa majalisar dinkin duniya barazanar kotu kan kudin da suke kashewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

AIT ta ce Ministar ta ba da wa’adin wata daya ga majalisar ta yi bayanin inda ta kashe duk kudin da ta karbo da sunan za ta taimaki Najeriya.

Kara karanta wannan

Matakan gaggawa 10 da gwamnatin Tinubu ta dauka daga jin za a shirya zanga zanga

2. Yunkurin hana aure a Neja

An yi ta surutu lokacin da aka ji Kennedy-Ohanenye ta shigar da kara a kotu domin hana aurar da wasu marayun ‘yan mata a jihar Neja.

Shugaban majalisar dokokin Neja ya yi niyyar aurar da yaran, a karshe dai an shawo kan sabanin da aka samu tsakanin bangarorin.

3. Minista ta ba mata shawarar zaman aure

Bayan zancen aurar da marayun jihar Neja, akwai lokacin da minister tarayyar ta yi kira ga mata su yi shiru a gaban mazajensu.

Uju Kennedy-Ohanenye ta ce mata su yi tsit yayin gardama a gidan aure, The Cable ta rahoto cewa majalisa ta soki maganar ministar.

4. Zargin karkatar da kudin al’umma

Hon. Kafilat Ogbara ta fito ta yi zargin cewa wasu kwamitoci a majalisar wakilai su na binciken ministar mata a kan karkatar da dukiya.

Ministar ta musanaya wadannan zargi masu nauyi, daga ciki har da kashe N45m ranar bikin sabuwar shekara, a karshe ta kai kara gaban kotu.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro ta jero mutanen da ake shirin kai wa hari a lokacin zanga zanga

5. Fadan ministar mata da majalisa

Duk da ta yi karar Hon. Kafilat Ogbara har tana neman N1bn a kotu, ministar ta zargi ‘yan majalisa da taso ta a gaba a kan wani bashi.

Uju Kennedy-Ohanenye ta ce saboda ta ki amincewa a ci wani bashin N500m ne ‘yan majalisar tarayya suka hana ta sakat ba komai ba.

6. Maulidin mijin Minista

Kafin ta gyara zama da kyau a ofis aka ji ministar matan kasar za ta shiryawa mijinta, Cif Kennedy Ohanenye bikin kara shekara a duniya.

Leadership ta je Transcorp Hilton, Abuja inda aka shirya za a yi bikin a lokacin, amma aka fahimci an fasa yin bikin ko dai an canza wuri.

Sanata ya debo ruwan dafa kan shi

Ku na da labarin yadda kalaman Sanata Ali Ndume su ka hada shi fada da majalisar dattawa da gwamnatin APC da ke karkashin Bola Tinubu.

Saboda Sanata Ali Ndume ya ce an katange Tinubu, an hana shi ya saurari gaskiya ne ya rasa kujerarsa a majalisa wanda hakan ya jawo surutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng