“Lokacin Yiwa Gwamnatin Tinubu Hisabi Bai Yi Ba,” Sakon Minista Ga Masu Zanga Zanga
- Karamin ministan albarkatun ruwa, Barista Bello Goronyo, ya yi magana kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa daga 1 ga Agusta
- Barista Bello Goronyo ya ce bai kamata 'yan Najeriya su yiwa Tinubu alkalanci tun yanzu ba inda ya ce shekara daya ta yi kadan
- A zantawarmu da wasu 'yan Najeriya kan wannan magana ta karamin ministan, sun ce lokaci ne ya yi da gwamnati za ta saurare su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Karamin ministan albarkatun ruwa, Barista Bello Goronyo, ya roki wadanda suka shirya zanga-zangar yunwa da su janye matakin da suka dauka.
Barista Bello Goronyo ya bayyana cewa bai kamata a fara yiwa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu hisabi daga yin shekara daya a mulki ba.
Karamin ministan ya bayyana hakan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki da gwamnatin jihar Sokoto ta kira kan zanga-zangar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shekara 1 ya yi kadan" - Minista
Barista Goronyo ya yi zargin cewa wadanda suka shirya zanga-zangar ba shugaban kasa suke hari ba, illa dai suna son kassara kasar ne.
A cewar ministan:
“Wadannan mutanen sun dauko kwangilar tada zaune tsaye a kasar nan. Ba wai shugaban kasa suke hari ba, suna harin kasarmu ne gaba daya.
“Shugaban kasa ya riga ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tukuru domin gyara matsalolin kasar. Don haka shekara daya da wata biyu sun yi kadan a yi masa alkalanci."
A cewar Barista Goronyo, gwamnatin Tinubu na yin duk mai yiwuwa domin kawar da yunwa da rashin tsaro a kasar.
Zanga-zanga: Minista ya roki matasa
Bello Goronyo ya yi kira ga matasan Arewa da su sake duba batun zanga-zangar da suke shirin yi, yana mai jaddada muhimmancin hadin kai wajen shawo kan kalubalen da ake fuskanta.
Jaridar Vanguard ta ruwaito karamin ministan na cewa Najeriya na bukatar jajurcewar 'yan Najeriya a irin wannan mawuyacin hali da kasar take ciki.
Goronyo ya ci gaba da cewa rattaba hannu kan dokar hukumar ci gaban Arewa maso Yamma shaida ce ta sadaukar da kan Shugaba Tinubu ga ci gaban yankin.
'Yan Najeriya sun yiwa minista martani
A zantawarmu da wasu daga cikin 'yan Najeriya kan maganar karamin ministan, Bashir Mashasha mazaunin Kaduna ya ce hakurin da aka yi tun bayan janye tallafin mai ya isa haka.
Bashir Mashasha ya ce lokaci ne ya yi da ya kamata gwamnati ta saurari bukatun 'yan kasar, ta janye tallafin mai ta kuma samar da hanyoyin rage farashin abinci.
Wani mai aikin faci a kan titin sha tale-talen Nnamdi Azikwe da ke Kaduna, Babangida Fifa, ya ce ma damar aka fita zanga-zanga shi ma zai rufe kasuwarsa ayi da shi.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta manta cewa talakawa ne suka tsaya kan layi komai tsananin zafin rana suka zabeta, amma yanzu talakawan ne ke shan bakar azaba.
Minista ya fadi muhimmancin mulkin Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa ministan ayyuka, David Umahi, ya ce da yanzu Najeriya ta karasa lalacewa idan da ubangiji bai ba Bola Tinubu nasara ba a zaben 2023.
Mista David Umahi ya ce kasancewar Bola Tinubu shi ne shugaban kasar Najeriya a wannan 'mawuyacin hali' ya sa kasar ba ta lalace ba.
Asali: Legit.ng