Bola Tinubu Ya Gano Masu Ɗaukar Nauyin Zanga Zanga, Ya Faɗawa Matasa Gaskiya
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙara yin tsokaci kan masu ɗaukar nauyin zanga-zanga da ake shirin yi a watan da ke tafe
- Bola Tinubu ya bayyana cewa masu ɗaukar nauyin ba mazauna ba ne kuma suna shirya komai tare da tunzura mutane daga ƙasashen ketare
- Shugaba Tinubu ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin Malaman Addinin Musulunci a Aso Villa ranar Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi iƙirarin cewa masu ɗaukar nauyin zanga-zangar da ake shirin yi ba su ƙishin Najeriya.
Tinubu ya bayyana haka ne ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa yayin da ya karɓi bakuncin Malaman Addinin Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau.
Sai dai shugaban ƙasar bai bayyana sunaye da bayanan masu ɗaukar nauyin zanga-zangar ba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya faɗi masu ɗaukar nauyin zanga-zanga
Shugaba Tinubu ya ce masu zugawa da matsa lamba dole sai an yi wannan zanga-zangar suna da fasfon wasu ƙasashen kuma ta intanet suke yin tarukansu.
"Masu ɗaukar nauyin zanga-zangar nan ba su kaunar Najeriya, babu sauran ɓurɓushin kishin ƙasa a zuƙatansu, ba su san komai ba game da zama ɗan ƙasa.
"Su na da katin zama a wasu kasashen ƙetare, daga can suke kitsa komai ta intanet. Ba mu son abin da ya faru a Sudan ya faru a Najeriya.
"Batu ne na yunwa ba jana'iza ba, dole mu yi taka tsan-tsan, mu san wasan da muke takawa a siyasa, mu kauce wa siyasa ƙiyayya da gaba. Ta intanet suke yin taruka suna ƙara tunzura mutane."
- Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa duk zanga-zangar da nufin nuna fushi da ƙiyayya, tana iya riƙeɗewa zuwa tashin-tashina kuma ta jawo koma baya a kasa, Daily Trust ta rahoto.
Malamai sun roƙi matasa su janye zanga-zanga
A wani rahoton kun ji cewa Malaman addinin Musulunci a Najeriya sun isar da koken talakawa ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Villa ranar Alhamis
Bayan ganawa da Tinubu, malaman sun roƙi ƴan Najeriya musamman matasa su haƙura sun janye zanga-zangar da suke shirin yi a watan Agusta
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng