A Kara Hakuri, Tattalin Arziki Na Dab da Gyaruwa: Abin da Tinubu Ya Fadawa Sarakuna
- Shugaba Bola Tinubu ya ba 'yan Najeriya tabbacin cewa yana aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin kasar, kuma ana samun nasara
- Shugaban kasar wanda ya yarda cewa akwai matsin rayuwa a kasar ya ce tattalin arzikin Najeriya na hanyar farfadowa sannu a hankali
- Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da sarakunan gargajiya inda ya roke su da su wayar da kan al'umma kan manufofinsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A yayin da ya yarda da cewa ana fama da matsin rayuwa, Shugaba Bola Tinubu ya ce tattalin arzikin Najeriya na kan hanyar farfadowa sannu a hankali.
Shugaba Tinubu ya kuma tabbatarwa ‘yan kasar cewa gwamnatinsa za ta kara bullo da tsare tsare a cikin kwanaki masu zuwa domin biyan bukatun su.
Ya bada wannan tabbacin ne lokacin da ya gana da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis, kamar yadda fadar shugaban kasar ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya
Sarakunan gargajiya sun samu jagorancin Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, da Ooni na Ife, Mai Martaba Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar da sanarwa bayan taron.
Kalaman shugaban kasar sun biyo wata zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki a fadin kasar nan da aka shirya yi a ranar 1 – 15 ga Agusta, 2024.
Tinubu ya ba 'yan Najeriya tabbaci
Taron na ranar Alhamis na daya daga cikin kokarin da gwamnatin tarayya ta yi a baya-bayan nan na hada kai da masu ruwa da tsaki domin dakile abin da ta ce 'shirin tayar da husuma.'
Tinubu ya ce zai ci gaba da bayyana sauye-sauyen tattalin arziki da alfanunsa ga al’ummar kasar, inda ya ce a shirye yake ya tattauna da kowa kan ci gaban kasar.
Don haka ya bukaci iyayen kasar (sarakuna) da su wayar da kan ‘yan kasa kan hakikanin kudirin gwamnati na cika alkawuran da ta dauka na kawo sauyi.
Tinubu ya musanta ana juya akalarsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce babu wasu 'yan ba ni na iya da ke juya akalar gwamnatinsa ko kuma masu gurgunta tattalin arziki.
Shugaba Tinubu ya ba da tabbacin cewa duk kudin da ya kashe a yakin zabensa sun fito daga aljihunsa ne don haka babu wanda zai bude masa ido a sha'anin mulkinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng