'Cabals': Masu Karfin Fada Aji Ke Juya Gwamnatin Tinubu? Shugaban Kasa Ya Fadi Gaskiya
- Shugaba Bola Tinubu ya ce babu wasu masu fada aji da aka fi sani da 'cabals' a turance da za su yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa
- Shugaban kasar ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba ta fada hannun wani kusa ba kuma babu bashin wani a kudin yakin zabensa
- Tinubu ya kara da cewa ubangiji ne kawai ya kudurta zai ci zabe, sai kuma jajircewa da gudunmuwar da ya samu daga 'yan Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa babu wasu masu fada aji (cabals) ko 'yan bani na iya da suka yi kaka gida a lamuran gwamnatinsa.
Hakazalika, shugaban kasar ya ce bai karbi kudin kowa ba a lokacin da yake yakin neman zabensa domin duk abin da aka kashe ya fito ne daga aljihunsa.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Tinubu ya fadi hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar malaman addinin Musulunci, karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Da kudina na yi yakin zabe" - Tinubu
Tinubu ya jaddada cewa shi ne ya dauki nauyin yakin neman zabensa, ba tare da wata tangarda ko bashi ga daidaikun mutane ko hukumomi ba.
Ya danganta nasarar zabensa ga yin ubangiji, yin tsari mai kyau da kuma goyon baya daga 'yan Najeriya.
Shugaban kasar ya kuma shaida cewa babu wani dan na iya ko wani mai kudi da ya dauki nauyinsa, ya yi amfani da dukiyarsa ne a lokacin.
Tinubu ya nuna muhimmancin 'takawa' wajen yaki da cin hanci da rashawa. Ya nemi da a mayar da hankali wajen ganin goben kananan yara ta yi kyau a Najeriya.
"Zanga-zanga na da matukar illa" - Tinubu
Shugaban kasar ya yi gargadin cewa zanga-zangar da aka yi ta da bacin zai da tsana na kaiwa ga tashin hankali da kuma jawowa kasar koma baya, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ya kuma jaddada cewa zai sake bullo da wasu shirye-shirye da za su kawo sauki ga rayuwar talaka da marasa galihu inda ya ce akwai shirin bashin karatu, sana'o'i da ke a kasa.
Shugaban kasar ya zargi wadanda ke ingiza matasa su yi zanga zanga da zama 'yan kasa marasa kishi, masu son ganin kasar ta shiga 'halin ha ula'i'.
"Ni ma na yi zanga-zanga a baya" - Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ce shi ma ya yi zanga-zanga a lokacin mulkin soja, amma bai shiga zanga-zanga ta tashin hankali ba.
Yayin da ya ce zanga-zanga 'yancin 'yan Najeriya ce, shugaban kasar ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci zanga-zangar da za ta zamo rigima ko jawo rusa dukiya, lafiya ko kisan jama'a ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng