Aso Villa: Wata sabuwar guguwa na kokarin yi wa 'Cabals' juyin mulki

Aso Villa: Wata sabuwar guguwa na kokarin yi wa 'Cabals' juyin mulki

Wata sabuwar mulki mai karfi ta bulla a fadar shugaban kasa wacce ke kokarin ture ikon 'miyagu' wadanda aka fi sani da 'Cabals".

Tun bayan kwanciya rashin lafiya da rasuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Mallam Abba Kyari, komai bai koma daidai ba ga wadanda ake zargin suna juya kasar nan.

Bayan sauyawa babban sakataren gidan gwamnati, Jalal Arabi wurin aiki, an janye shaidar shiga fadar ga wani babba daga cikin masu juya kasar nan.

Hakan ne yasa mai tarin ikon ke zuwa fadar tare da bukatar shiga ta hanyar da ta dace kamar yadda kowa yake yi, jaridar The Nation ta wallafa.

Sauya wa sakataren wurin aiki yasa masu karfin ikon basu da labaran abubuwan da ke faruwa a fadar kamar yadda suka saba samu.

Wata majiya ta sanar da SENTRY cewa, "Akwai wasu sabbin masu iko da ke bayyana kuma kowa na taka-tsan-tsan da su don gudun abinda zai iya faruwa."

Karin bayani na nan zuwa nan da mako mai zuwa.

Aso Villa: Wata sabuwar guguwa na kokarin yi wa 'Cabals' juyin mulki

Aso Villa: Wata sabuwar guguwa na kokarin yi wa 'Cabals' juyin mulki. Hoto daga jaridar The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Shekau ya samu taimakon Euro miliyan 5 daga wata kungiya: Gaskiya ta al'amari ya bayyana

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel